Mutane da dama sun mutu bayan tashin gobara a tashar jiragen ruwa a Fatakwal
Har zuwa yanzu dai ba a san musabbababin gobarar ba.
Jiragen kwalekwale da dama makare da kaya sun kone sakamakon wata gobara da ta tashi a babbar tashar jiragen ruwa ta Nembe-Bonny da ke birnin Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.
Ana dai fargabar gobarar ta yi sanadiyyar lakume rayukan mutane, ciki har da wasu yara biyu da ma wasu da ba a kai ga tantance adadinsu ba.
- An bukaci gwamnatin Kano ta mayar wa da Jami’ar Maitama Sule kadarorinta
- Sudan: Sojoji sun dawo da fira Minista Hamdok kan mulki
Har zuwa yanzu dai ba a san musabbababin gobarar ba, amma ana kyautata zaton wani jirgi dauke da kalanzir ne ya fara kamawa inda daga bisani wutar ta kama wasu sassan tashar.
Sai dai wata majiyar ta shaidawa wakilinmu cewa mutanen da ke dillancin kalanzir ta haramtacciyar hanya ne suka yi musabbabin tayar da gobarar.
“Musabbabin gobarar yana da alaka da masu siyar da man fetur ba bisa ka’ida ba a tashar, musamman a jirgin da gobarar ta tashi, daga baya wutar ta kama sauran jiragen ruwa da ke tashar wanda ya yi sanadiyyar konewar kayayyaki na miliyoyin Naira,” inji shi.
Ko da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Nnamdi Omoni bai samu hakan ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Dama dai tashar ta Nembe-Bonny ta yi kaurin suna wajen harkalla da cinikin man fetur ba bisa ka’ida ba.