Yawancin mutane ba su fahimci ƙudirin dokar haraji ba – Barau
Sanata Barau ya ce an bai wa jama’a damar yin sharhi kan ƙudirin dokar harajin.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana cewa mutane da dama, ciki har da wasu ’yan majalisa ba su fahimci yadda ƙudirin gyaran dokar haraji yake ba.
Barau, ya ce an amince wa dokar zuwa karatu na biyu ne domin a bai wa al’umma damar tofa albarkacin bakinsu.
- Gwamnatin Kano ta mayar wa Jami’ar Yusuf Maitama tsohon sunanta
- Isra’ila ta soma saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta a Lebanon
Ƙudirin dokar ya haifar da cece-kuce, musamman a Arewacin Najeriya, inda ake ganin za ta ƙara jefa yankin cikin mawuyacin hali na tattalin arziƙi.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwa kan dokar a wata hira da ya yi da BBC Hausa, inda ya ce, “Idan har aka amince da dokar, gwamnoni za su fuskanci ƙalubale wajen biyan albashi.
“Abin damuwa ne yadda aka yi saurin wajen tattauna ta a majalisa.”
Da yake mayar da martani kan lamarin, Barau ya kare matakin, inda ya bayyana cewa, “Dole ne a bai wa dokar damar zuwa karatu na biyu domin a bai wa ’yan Najeriya damar yin sharhi da kuma yin tambayoyi.
“Wannan shi ne farkon mataki; yanzu kwamiti zai yi nazari sosai tare da karɓar shawarwari daga ƙwararru da kuma al’umma.”
Barau, ya jaddada cewa ba a yanke wata matsaya ba tukuna, inda ya ce ’yan majalisa suna kan bincike domin tabbatar da cewa dokar ba za ta cutar da al’ummar Najeriya ba.