Mutane da yawa sun fadi a jarabawar WAEC ta bana-Adenipekun

Babban ofishin hukumar shirya jarabawa ta kasashen Afirka ta Yamma wacce ake yi wa lakabi da WAEC ta fitar da sakamakon zabe na zagon watanin Janairu da Fabarairu inda wadanda suka zauna jarabawar dubu daya da 937 wanda suka kai kashi 17 da digo 13 cikin dari ne suka sami nasara a darussa biyar da […]

Mutane da yawa sun fadi a jarabawar WAEC ta bana-Adenipekun

Babban ofishin hukumar shirya jarabawa ta kasashen Afirka ta Yamma wacce ake yi wa lakabi da WAEC ta fitar da sakamakon zabe na zagon watanin Janairu da Fabarairu inda wadanda suka zauna jarabawar dubu daya da 937 wanda suka kai kashi 17 da digo 13 cikin dari ne suka sami nasara a darussa biyar da suka hada da lissafi da harshen Turanci
 
Da yake bayyana sakamakon jarabawar jiya a Legas, shugaban ofishin cibiyar shirya jarabawar na Najeriya, Olu Adenipekun ya bayyana rashin jin dadinsa da sakamakon jarabawar inda ya ce abin da ban mamaki idan aka kwatanta da sakamakon jarabawar ta shekara 2018 inda fiye da kashi 26 cikin dari suka samu nasara a darussa biyar ciki har da lissafi da turanci.
 
Adenipekun ya bayyana cewa yayin da mutum dubu 11 da 721 suka yi regista mutum dubu 11 da 307 ne kawai suka rubuta jarabawar.
 
Ya bayyana cewa cikin adadin da suka rubuta jarabawar kmimanin kashi 17 da digo 13 cikin dari ne suka samu nasara.