Mutane dubu 500 ne suka yi kaura daga garin Mosul

Akalla mutane dubu 500 suka fice daga gari na biyu mafi girma a kasar Iraki, Mosul bayan da masu kishin Islama da ke gwagwarmaya da makamai domin kafa daular Musulunci suka ci gaba da mamaye yankunan garin.Hukumoni a kasar sun bayyana cewar ’yan gwagwarmayar masu yunkurin kafa kasar Iraki mai bin tafarkin Islama watau (ISIL), […]

Mutane dubu 500 ne suka yi kaura daga garin Mosul
Mutane dubu 500 ne suka yi kaura daga garin Mosul

Akalla mutane dubu 500 suka fice daga gari na biyu mafi girma a kasar Iraki, Mosul bayan da masu kishin Islama da ke gwagwarmaya da makamai domin kafa daular Musulunci suka ci gaba da mamaye yankunan garin.
Hukumoni a kasar sun bayyana cewar ’yan gwagwarmayar masu yunkurin kafa kasar Iraki mai bin tafarkin Islama watau (ISIL), sun kuma kwace garuruwa da birane a lardunan Kirkuk da Salaheddin.
An kiyasta cewa kusan mayakan ISIL 1300 ne, a ranar Talata suka karbe iko da garin da kuma filin jirgin saman birnin. Mayakan sun kai hari gine-ginen gwamnati da gidajen talabijin da kuma bankuna. Sun kuma kai hari lardin Ninebeh, inda suka salami fursinoni fiye da 2000.
Amurka dai ta yi kira ga Firaministan kasar, Nouri al-Maliki wanda dan Shi’a ne da ya hada hannu tare da ’yan Sunni mara sa rinjaye domin farfado da doka da oda a yankin.
Birnin Mosul ya na da yawan jama’a da suka kai miliyan biyu, kuma ta nan ne ake fitar da galibin mai fetur din kasar zuwa kasashen ketare. A shekaranjiya Laraba, Shugaban kasar ya yi shelar aiyana dokar ta baci bayan gwamnatinsa ta rasa iko a garin da kuma wani bangaren na landir Ninebeh.