Mutane na murnar rufe otel din Mbanefo Holiday a Kano
Mutane da dama sun nuna farin ciki da murna kan rufe otel din Mbanefo da Gwamnatin Jihar Kano ta yi. Fitacen otel din na Mbanefo Holiday Inn da ke Lamba 42 zuwa 45 a kan Titin Abeokuta a Unguwar Sabon Gari a birnin Kano ana zarginsa da gudanar da fataucin mutane da aikata wasu abubuwa […]
Mutane da dama sun nuna farin ciki da murna kan rufe otel din Mbanefo da Gwamnatin Jihar Kano ta yi.
Fitacen otel din na Mbanefo Holiday Inn da ke Lamba 42 zuwa 45 a kan Titin Abeokuta a Unguwar Sabon Gari a birnin Kano ana zarginsa da gudanar da fataucin mutane da aikata wasu abubuwa da suka saba wa shari’a.
A lokacin rufe hotel din wanda aka yi shi a karkashin jagorancin wani babban kwamiti da ya kunshi jami’an tsaro na ’yan sanda da na Hukumar Shigi da Fici da na Hukumar Hisba da ma’aikatan Hukumar Kula da Yawon Bude-Ido da na Hana Fataucin Mutane da Kananan yara an samu nasarar kama akalla mutum 30.
Yayin da yake zantawa da manema labarai, Shugaban Hukumar Kula da Yawon Shakatawa da Yawon Bude-Ido Alhaji Abdullahi Mu’azu Gwarzo ya ce Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayar da umarnin rufe otel din bayan samun rahoto daga ofishin Sakataren Gwamnati kan abubuwan da otel din ke yi da suka saba wa shari’a.
Shugaban ya ce rahoton da Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya samu ya nuna cewa watannin da suka gabata Hukumar Shigi-da-Fici ta Kasa a Jihar Knao ta kama akalla baki 14 ’yan asalin kasashen Kamaru da Chadi da ake zargin sun shigo jihar ce don hutawa a hanyarsu ta gudanar da fataucin mutane wanda hakan ya saba wa sashe na 44 (h) i-iii na Kundin Shari’ar Hukumar Kula da Shigi-da- Fici.
Aminiya ta gano cewa sauran ayyukan assha da ake zargin otel din da aikatawa sun hada da bautar da kananan yara da sanya su yin karuwanci inda ake yaudarar kananan yara zuwa otel din, wadanda laifuffuka ne da suka saba wa dokokin Hukumar Hana Fataucin Mutane ta Kasa da kuma na Hukumar Hisba ta Jihar Kano.
A cewar Abdullahi Gwarzo a watannin baya hukumarsa ta gayyata tare da yi wa hukumar gudanarwar otel din gargadi kan abubuwan da suke faruwa a otel din, inda suka nemi afuwa tare da alkawarin daukar matakan gyara. Sai dai a cewarsa daga wancan lokaci maimakon a samu saukin lamura sai suka kara tabarbarewa.
Har ila yau hukumar ta zargi otel dn da kin biyan kudin haraji na tsawon shekara biyu sai dai biyan wani bangare na abin da ya shafi hukumar.
Shugaban ya yi kira ga masu otel-otel da ke jihar su tabbatar suna bin dokokin da aka shimfida wajen gudnaar da otel kasancewar Gwamnatin Jihar Kano tana bibiyar ayyukansu tare da daukar tsauraran matakai a kan duk wanda ya karya dokokinta.
Yayin da yake mayar da martani a madadin otel din, Manajan otel din Mista Boniface Anayochukwu ya ce ya yi rajista da Hukumar Kula da Yawon Shakatawa da Yawon Bude-Ido sai dai daga baya an kwace lasisin inda kuma aka yi masa umarnin ya sake neman yin rajista. Ya ce yana biyan duk wasu kudade da ke kansa ga wannan hukuma.
Mista Boniface ya yi kira ga gwamnati ta bude masa otel din lura da cewa otel din ya dauki tsawon shekara 40 yana bayar da gudunmawarsa ga bunkasa tattalin arzikin Jihar Kano, inda ya yi alkawarin bin dokokin da gwamnatin ta shimfida sau da kafa.