Mutane na sallah sahu guda da maguna a Turkiyya
Mutane na sallah sahu guda da maguna a masllacin birnin Istambul da ke kasar Turkiyya, inda Limamin masallacin Aziz Mahmud Hudayi, Imam Musdafa Efe yake bai wa maguna mafaka tun bara. Yana bayar da mafakar ne ga magunan domin su ji dumi a lokacin sanyi.Limamin na matukar bai wa maguna kariya tare da kyautata musu, […]
Mutane na sallah sahu guda da maguna a masllacin birnin Istambul da ke kasar Turkiyya, inda Limamin masallacin Aziz Mahmud Hudayi, Imam Musdafa Efe yake bai wa maguna mafaka tun bara. Yana bayar da mafakar ne ga magunan domin su ji dumi a lokacin sanyi.
Limamin na matukar bai wa maguna kariya tare da kyautata musu, inda ya saba kyauta musu a masallacinsa.
Wadannan bakin magunan da limamin ke Tarawa, yana ba su kyakkyawan wurin zama. Kyanwa na samun kariya a wannan masallaci, har ma wasu na kawo ’ya’yan su daya bayan daya. Kai akwai magunan da kan hau kan mumbari, inda Imam Efe ke yin wa’azi. “Kyanwa ta samu tausasawa da jinkan zuciya,” kamar yadda Efe ya rubuta a shafin facebook din sa.