Mutane na tururuwa wurin da aka ce an samu ‘ruwan magani’
Mazaunan wani yanki a cikin Rigasa ta Karamar Hukumar Igabi da ke jihar Kaduna sun yi tururuwar dibar wani ruwa da ke bulbulowa daga kasa, wanda suka ce wai yana maganin cututtuka daban-daban. Rahotanni na nuna cewar ruwan ya kusan wata guda yana fitowa ba tare da kowa ya san sirrin da ke cikinsa ba. […]

Mazaunan wani yanki a cikin Rigasa ta Karamar Hukumar Igabi da ke jihar Kaduna sun yi tururuwar dibar wani ruwa da ke bulbulowa daga kasa, wanda suka ce wai yana maganin cututtuka daban-daban.
Rahotanni na nuna cewar ruwan ya kusan wata guda yana fitowa ba tare da kowa ya san sirrin da ke cikinsa ba. Ruwan ya fito ne a Rigasa Hiland, wata unguwar talakawa da babu mutane sosai.
Bincike ya nuna cewa inda ruwan ke bulbulowa magudanar ruwa ce wadda ta dade ruwa ba ya bi ko taruwa sai a kwanakin nan.
Da Aminiya ta ziyarci unguwar ta tarar da magidanta da tsofaffi mata da ’yan mata da yara, musamman matasa suna dibar wannan ruwa. Wasu na diba cikin manyan goruna, wasu kuwa sha suke yi.
A cewar masu dibar ruwan, wai yana maganin cututtuka masu yawa, kuma wai wani makaho ne ya wanke fuskarsa da ruwan daga nan ya fara gani; sai mutane ke zuwa neman tabaraki.
Aminiya ta bukaci ganin makahon, amma abin ya ci tura. Wasu dai kawai suna dibar ruwan ne suna sha don an ce yana maganin cututtuka, amma ba su san wani makaho ba, a cewar Mohammadu Eazy layin Makarfi a Rigasa.
Game da tsaftar ruwan, sai ya ce wai a ganinsa ruwan na da tsafta kasancewar fari ne ba ja ba.
daya daga cikin matasan da ke taimaka wa mutane dibar ruwan, mai suna Salisu, ya ce: “Gaskiya ni ba zan iya cewa komai ba, saboda ba ni da cikakken bayani akan wannan ruwa. Amma kamar yadda ka ji kowa na fadi wai wani mutum ne ya wanke fuskarsa ya kuma samu lafiya daga nan ne mutane suka rika tururuwa zuwa dibar ruwan,” inji shi.
Dangane da abin hasafin diba, sai ya ce: “ Gaskiya ba a biyan ko sisin kwabo, amma dai idan mutum ya yi niyya yakan ba da sadaka ga masu kulawa da wajen,” inji shi.
Wata mata da goyo wacce taki ta ambaci sunanta, ta shaida wa Aminiya cewa ita kam taga amfanin shan wannan ruwa. kawar matar ta bayana wa Aminiya cewa, ita ma dai tana sha ne saboda an ce yana magani. “To, mu dai muna sha ne tun da an ce yana magani. Kuma ina ganin yana aiki a jiki kamar yadda aka ce”
Bayanai sun nuna wai mutane na zuwa har daga wasu unguwannin dake nesa suna dibar wannan ruwa suna tafiya da shi suna sha su kuma yi wanka da shi.
Aminiya ta tuntubi Shugaban kungiyar Likitoci na Jihar Kaduna, Likita Usman Baffa Aliyu, domin jin ra’ayinsa akan wannan zance inda ya gargadi mutane da su daina bari ana rudarsu.
A cewarsa, in ban da ruwan zamzam da ke Saudiyya, wanda musulunci ya nuna yana maganin cututtuka babu wani ruwa dake iya warkar da wata cuta.
Likitan ya bukaci mutane su tashi tsaye wajen neman ilimi a wajen likitoci a kan cututtukan da ke damunsu.
Ya kuma nuna damuwarsa kan masu ikirarin bada magunguna da suke cewa wai suna warkar da manyan cututtuka.
“Mafi akasarin lokuta sai sun bata lokaci wajen shan irin wadannan magunguna marasa asali, sannan su zo asibiti. Daga karshe babu abin da likita zai iya yi musu. Saboda haka muna kira a garesu da su tabbatar suna zuwa asibiti yin bincike a maimakon bata lokacinsu wajen shan irin wannan abubuwa,” inji likitan a zantawarsu da Aminiya ta wayar tarho.