Mutane sun ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi a Bauchi

Masu sanyan ido kan zaɓen sun ce mutane ba su fito sosai domin kaɗa ƙuri’a ba.

Mutane sun ƙi fita zaɓen ƙananan hukumomi a Bauchi

An samu ƙarancin masu kaɗa ƙuri’a a wajen zaɓen ƙananan hukumomin da ke gudana a Jihar Bauchi.

Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa zaɓen a ƙananan hukumomin Bauchi, Dass da kuma Tafawa Balewa, sun samu naƙaso yayin da mutane suka ƙi fitowa domin kaɗa ƙuri’a.

An fara zaɓen a wurare irin su Makarantar Sakandaren Gwallameji, Kofar Sarkin-Gwallameji, Makarantar Sakandaren Sa’adu Zungur da GSS Baba-Sidi, sai dai babu masu jefa ƙuri’a ba da yawa.

Masu jefa ƙuri’a da suka halarta sun hau layi cikin nutsuwa hankali, inda suka yi dakon zuwan jami’an zaɓe, wanda hakan ya bai wa jami’an hukumar damar gudanar da shirye-shiryensu cikin lumana.

NAN, ya ruwaito cewa an tura isassun jami’an tsaro a wuraren da ake gudanar da zaɓen, yayin da mafi yawan mazauna yankunan ke ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Wani rukuni na masu sanya ido kan zaɓen, sun bayyana jin daɗinsu game da yadda ake gudanar da zaɓen cikin lumana.

Mista Mamman Eri, babban mai sanya ido, ya yaba wa masu zaɓe, ma’aikatan zaɓe, da jami’an tsaro kan yadda aka gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali.

Eri, wanda shi ne Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kogi (SIEC), ya jagoranci sauran Shugabannin Hukumar Zaɓe na Jihohi wajen sanya ido kan yadda zaɓen ke gudana.

“Mun zagayawa wurare da dama, zaɓen na gudana cikin kwanciyar hankali. Mutane suna gudanar al’amuransu yadda ya kamata, kuma akwai wakilan jam’iyyun siyasa a wuraren zaɓen sun,” in ji Eri.

Kashim Shettima zai jagoranci tawagar Nijeriya a taron MDD

NECO ta fitar da sakamakon jarrabawar 2024

Kano: Abba ya rusa ciyamomin riko

An haramta wa ma’aikatan Asibitin Tarayya yin ‘kirifto’ a wurin aiki