Mutane Sun Fasa Rumbun Abincin Gwamnati A Jihar Kebbi
Da ƙarfin tuwo suka shiga suka wawushe kayayyakin da ke rumbun ajiyar gwamnati da wasu shagunan ’yan kasuwa.
Waɗansu mutane da kawo yanzu ba a bayyana kama ko ɗaya daga cikinsu ba sun fasa rumbun abincin gwamnati a Jihar Kebbi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa, an fasa rumbun abincin da ke Unguwar Bayan Kara a Birnin Kebbi a ranar Lahadi da ta gabata.
Mutanen da suka fasa rumbun sun fi galaba ne a kan jami’an tsaron da aka ɗora wa alhakin tsare rumbun da gwamnati ta shake da kayan abinci.
An bayyana cewa bayan Rumbun Gwamnati da ka fasa, mutanen sun wawushe kayan abincin da ke makare a wata mota da ta lalace a kan hanya.
- Hajji: Gwamnonin Kogi, Kebbi da Kano sun tallafa wa maniyyata
- NAJERIYA A YAU: Mutuwar Zuciya Ce Ta Jefa Matasa Harkar Kirifto
Shugaban ’yan kasuwar Bayan Kara dake Birnin Kebbi Muhammadu Gwadangwaji ya ce, ba iya Rumbun Gwamnati mutane suka fasa ba.
A cewarsa, an fasa wasu shagunan ’yan kasuwa an kuma cinna wa wasu wuta, duk da irin ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi.
“Duk da cewa jami’an tsaro sun yi ta harba bindiga da barkonon tsohuwa a cikin iska, mutanen ba su hakura ba.
“Da karfin tuwo suka shiga suka yi awon gaba da kayayyakin da ke rumbun ajiyar gwamnati da wasu shagunanmu.”
Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan jihar Kebbi Nasir Idris; Ahmed Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “abin takaici”.
Ya bayyana cewa: “Tun da farko an samu wasu ɓata-gari sun kai hari kan kayan abinci da Dangote ya aiko jiharmu domin rabawa jama’a kafin daga baya su karasa ma’ajiyar gwamnati su kwashe abin da ya saura.
“Irin wannan lamari bai taba faruwa a Kebbi ba. Kayayyakin abincin da suka wawashe na daga cikin kayan abincin da gwamnatin jihar ta siya domin raba wa al’umma.
“Gwamnati ta raba hatsi da ya kai sama da na Naira biliyan 5, cikin manyan motoci sama da 200.
“Abin bakin ciki ne, wannan abin da haka kawai wasu su kutsa cikin rumbun ajiyarmu su sace abin da yake na mutanen jihar ne baki ɗaya.
Ya ce, gwamnati ta ɗauki matakin kare ma’ajiyar ta domin hana afkuwar irin haka anan gaba.
Aminiya ta nemi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Nafiu Abubakar, domin jin ta bakinsa, amma bai amsa kiran wayar ba.