Mutane sun fi neman laifin ’yan fim —Darakta Abdulmumini Tantiri
Fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, wanda ya dade ana damawa da shi, Iliyasu Abdulmumin Maisango, wanda aka fi sani da Tantiri ko Dankasa ya bayyana takaici cewa mutane sun fi mayar da hankalinsu kan neman laifukan ’yan fim sama da alherinsu. Iliyasu Abdulmumin ya yi wannan jawabin ne saboda yadda a cewarsa mutane suka ki […]
Fitaccen darakta a masana’antar Kannywood, wanda ya dade ana damawa da shi, Iliyasu Abdulmumin Maisango, wanda aka fi sani da Tantiri ko Dankasa ya bayyana takaici cewa mutane sun fi mayar da hankalinsu kan neman laifukan ’yan fim sama da alherinsu.
Iliyasu Abdulmumin ya yi wannan jawabin ne saboda yadda a cewarsa mutane suka ki yada gina Masallacin jaruma Hadiza Gabon ke yi, amma da a ce laifi ne, da ya karade kafofin sadarwa.
“Duk da cewa Musulunci ya yi hani da yada alfasha, ina ganin inda al’ummarmu suka fi karkata ke nan —Daga masu sanya wani abu, zuwa masu jawabi a kasan abin a kafafen yada labarai.
“Burinsu a ce dan film ko ’yar film sun yi laifi su yada a duniya da tsinuwa da la’anta.
“Abin mamaki wannan baiwar Allah Hadiza Gabon ta yi abin alheri kamar yadda kuke gani, na duba kafafen da suka yi suna wajen batanci da son yada laifin ’yan film ban ga sun yi wannan ba.
“Inda aka sanya dinma idan ka duba masu jawabi a kasa za ka ga mutane kalilan ne.
“Hakan ya sa na tambayi wasu masu sanya laifin ’yan film cewa yaya na ga ba ku sanya wannan abin alheiri ba? Sai suka ce mun wai ai tsakaninta da Allah ne.
“To shi laifin idan ’yan film sun yi, ‘ku suka yi wa? Na ga dai gara ka yada alheri da ka yada sharri, domin shi mai yada laifi cikin al’umma ya fi mai laifin kasanta.
“Annabi S.A.W ya ce ku fadi alheri ko ku yi tsit. Allah Ya saka da alheri, Malama Hadiza.”
Rahotanni suna nuna cewa Hadiza Gabon ta gina Masallacin ne a garin Kaduna.
View this post on Instagram