Mutane sun hana gina masallaci a garin su Edwin Clark

Mutanen qauyen Kiagbodo mahaifar tsohon Minista kuma Shugaban Qungiyar Mutanen Kudu maso Kudu da Tsakiyar Najeriya Cif Edwin Clark da ke Qaramar Hukumar Burutu  a Jihar Delta sun hana daya daga cikin ’yan asalin qauyen mai suna Malam Abubakar Korokeme gina masallaci a cikin gidansa. Al’ummar qauyen su kuma qeqashe qasa suka nuna qin yardarsu […]

Mutane sun hana gina masallaci a garin su Edwin Clark

Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa

Mutanen qauyen Kiagbodo mahaifar tsohon Minista kuma Shugaban Qungiyar Mutanen Kudu maso Kudu da Tsakiyar Najeriya Cif Edwin Clark da ke Qaramar Hukumar Burutu  a Jihar Delta sun hana daya daga cikin ’yan asalin qauyen mai suna Malam Abubakar Korokeme gina masallaci a cikin gidansa.

Al’ummar qauyen su kuma qeqashe qasa suka nuna qin yardarsu da ginin masallacin, inda suka ce ba za a gina masallaci a yankin nasu ba.

Al’ummar qauyen Kiagbodo sun yi zargin cewa idan aka gina masallaci a gidan, zai kasance mafakar Fulani makiyaya inda suka ce ba za su yarda a yi wa Fulani makiyaya mafaka ba, su zo suna tafka ta’asa da yi wa mata da yara fyade.

A ranar Lahadin da ta gabata ce wadansu matasan qauyen suka rushe sassan ginin masallacin tare da yin gangamin nuna rashin amincewarsu a gidan mutumin. Al’ummar qauyen Kiagbodo sun yi zama a ranar 26 ga Yulin da ya gabata inda mazansu da matansu suka ce, ba su yarda a gina masallaci a qauyen ba bisa hujjar  cewa ba za su yarda a yi wa batagari mafaka ba.

Sai dai Alhaji Abubakar Korekeme ya ce masallaci wuri ne na ibada wanda shi da ’yan uwansa Musulmi za su yi amfani da shi wajen gudanar da al’amuransu na ibada kamar yadda dokar qasa ta bai wa kowa ’yanci.

Ya ce, tun lokacin da ya fara aikin ginin masallacin ya yi ta samun barazana daga mutane da dama a  qauyen inda wadansu suka aike masa saqon ko dai ya rushe ginin ko su turo a rushe. Ya ce a wani zama da aka yi Shugaban Qaramar Hukumar Burutu, Mista Godknows Angele ya nanata wa mutane qauyen cewa yana da ikon ya gina masallaci a gidansa domin gudanar da ibada, inda ya ce babu wani aibu game da haka.

Amma a bangaren wani shugaban al’umma a qauyen Kiagbodo Mistake J.O Layefa ya qi amincewa da wannan batu, ya ce ba ya da masaniyar cewa Shugaban Qaramar Hukumar ya amince a ci gaba da ginin masallacin. “Ba haka ya fada mana ba, babu wata maganar tashin-tashina a nan, mutanen wannan yanki sun nuna ba sa son masallacin, mu kuma shugabancinmu yana tare da jama’a ne. Lokacin da muka yi zama a kan wannan batu tare da jama’ar gari da jami’an tsaro, Shugaban Qaramar Hukumar ya ce kamata ya yi mu saurari umarni daga Cif Edwin Clark wanda shi ne uban yankin, kuma a daidai lokacin da ake zaman sauraron umarninsa dole a daqatar da aikin ginin masallacin,” inji shi.

Alhaji Isa Clark qanen Cif Edwin Clark, wanda shi ma Musulmi ne ya nuna taqaicinsa bisa lamarin da ya alaqanta da tauye haqqin marasa rinjaye a qauyen. A wata takardar da ya rubuta a ranar 27 ga Agustan da ya gabata ya ce, wadansu mutanen qauyen da ke kiran kansu shugabannin yankin sun hada kai domin su cutar da Musulmin qauyen.  Ya ce yawancinsu da suke wannan yunquri sun jahilci tsarin  mulkin qasa na 1999.

Bayanai sun ce Shugaban Qaramar Hukumar ya ja hankalin jami’an tsaro da suka hada da DPO yankin su tabbatar sun daidai ta al’amuran tsaro a yankin domin samun wanzuwar zaman lafiya a yankin.