Mutane sun je kona cibiyar allurar rigakafin COVID-19

Ana neman wadanda suka kai wa cibiyar hari da abubuwan fashewa.

Mutane sun je kona cibiyar allurar rigakafin COVID-19

Cibiyar hada rigakafi na SII a lokacin da wata bogara ta tashi. (Tsohon hoto).

Jami’an tsaro na neman wasu mutane da suka kai hari da nufin kona wata cibiyar bayar da allurar rigakafin cutar COVID-19.

Akalla mutum uku ne jami’an tsaron suke name kan yunkurin na kona cibiyar allurar rigakafin COVID-19 din da ke Jihar Saxony ta kasar Jamus.

Ana zargin wasu mutum uku ne suka jefa kwalabe cike da makamashi a cikin ginin cibiyar allurar rigakafin cutar a garin Treuen da yammacin ranar Talata.

Wasu shaidu sun ce maharan sun kai wa cibiyar farmaki ne a cikin wata jar mota, amma har yanzu ba a ga alamar motar ba.

Mai magana da yawun ’yan sanda a garin ya ce karon farko ke nan da aka kai irin harin a a garin.

Sai dai ya bayyana cewa abin ya zo da sauki saboda bai yi barna ba sosai a cibiyar, hasali ma abubuwan fashewar ba su tashi ba.

A karshen watan Satumban da muke ciki ne ake sa ran rufe cibiyar da aka kai wa harin, tare da wasu cibiyoyin rigakafin 12 da ke Jihar ta Saxony