Mutane sun  kasa fahimtar ayyukan mazabun ’yan majalisa –  Kasimu Maigari

A yayin da ake zargin ana yi badakalar kan aikin mazabun ’yan majalisa, inda har Shugaban Kasa ya koka cewa aikin ya ci Naira tiriliyan daya cikin shekara 10, amma babu wani abu da za a nuna, Aminiya ta zanta da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Jalingo, Yoro da Zing daga Jihar Taraba, Alhaji Kasimu […]

Mutane sun  kasa fahimtar ayyukan mazabun ’yan majalisa –  Kasimu Maigari

Alhaji Kasimu Bello Maigari

A yayin da ake zargin ana yi badakalar kan aikin mazabun ’yan majalisa, inda har Shugaban Kasa ya koka cewa aikin ya ci Naira tiriliyan daya cikin shekara 10, amma babu wani abu da za a nuna, Aminiya ta zanta da dan Majalisar Wakilai mai wakiltar Jalingo, Yoro da Zing daga Jihar Taraba, Alhaji Kasimu Bello Maigari inda ya ce mutane sun kasa fahimtar ayyukan mazabun inda suke dauka ana mika musu kudin ne:

Yaushe ka fara harkar siyasa?

Ni dai hafaffen garin Zing ne a Jihar Taraba. Na fara shiga siyasa ce tun a 1999 lokacin da siyasa ta dawo inda na fara zama Magatakardan jam’iyya a unguwarmu. Na yi siyasar APP zuwa ANPP zuwa CPC ta Buhari, kuma ni ne na fara wannan jam’iyya a Jihar Taraba. Na zama babban mai karbar baki na Buhari a matsayinsa na dan takarar Shugabanci Kasa. Na kuma zama Shugaban Matasa na Jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Gabas, kafin in fito neman takarar dan Majalisar Tarayya don wakiltar kananan hukumomin Jalingo daYoro da  Zing inda Allah Ya ba ni nasara na shigo Majalisar Wakilai  a zaben da ya gabata.

Daya daga cikin abubuwan da ake korafi a kan ’yan majalisa shi ne ayyukan mazabu da suke ware wa kansu, me za ka ce?

Bayanin farko da zan yi shi ne, ba a bai wa dan majalisa ko Naira 10 da sunan wadannan ayyuka. Sabanin bayanan da suke fitowa musamman daga wajen ku ’yan jarida da kuke sanar da al’umma cewa ana ba mu kudinsu, muna ci, abin da ke faruwa shi ne, ana ware wa daukacin ’yan Majalisar Wakilai da suka fito daga jiha daya Naira miliyan dubu daya, wadda ake sa musu a cikin kasafi. Wannan kudi da ake warewa bai da bambanci a tsakanin jihohi masu wakilai  6 irin jihata ta Taraba da jihohi irin su Kano da ke da wakilai 24. Ka ga ke nan mu masu wakilai 6 mu ne muka fi samu, amma idan ka raba wannan kudi zuwa gida 6 aikin da za a yi wa wakili a yankin da yake wakilta ba zai wuce na Naira miliyan 166 ba. Idan kuwa wakilai ne daga Kano ka ga nasu kudin ba zai wuce Naira miliyan 41 ba, ga kowannensu. Wannan a kasafi ke nan, sai kuma kuma aiwatarwa. To har zancen nan da nake maka a yanzu ka ga dai muna karshen watan Nuwamba, amma har yanzu ba a saki ko kwabo ba daga wannan kudi. Kuma karshenta idan aka tashi sako kudin tsanani idan an yi kokari a ba da rabi. Ka ga ke nan mai jiran a ware masa Naira miliyan 166 karshe kudin zai koma ne Naira miliyan 83. Shi kuwa dan majalisa daga Kano da yake tsammanin Naira miliyan 41, a ware masa miliyan 20. To ba nan ma gizo ke sakar ba, kudin nan da ake zance, ba dan majalisa ake bai wa su ba. shi dai kawai zai zabi aikin da yake ganin yankinsa ya fi tsananin bukata ne kawai, sai a sa shi a cikin kasafi kudin mazabu, sannan idan an saki kudin sai ya je ma’aikatar da ke da alhakin yin wannan aiki.

Akwai zargin cewa ’yan majalisa na hada kai da ’yan kwangila, a jigine aikin a yi watandar kudin a tsakani, me za ka ce?

To idan har ana yin haka, ni ban kai ga ganowa ba, saboda watanni kadan na yi a majalisar nan kuma har yanzu ba a kai ga sako kudin bana ba na aikin mazabu.

Akwai masu cewa ’yan majalisa su tsaya wajen tsara dokoki da sanya ido kawai, sannan kasafin mazabu da ake ware musu a hada wa bangaren zartarwa, me za ka ce?

Masu fadin haka ba su san mene ne aikin dan majalisa ba. A yanzu haka a cikin kananan hukumomi uku 3 da nake wakilta, duk yadda za ka yi da bangaren zartarwa ba zai san wasu matsalolinsu ba, sai dai ni wakilinsu. Domin mu ne idanunsu, kuma idan so samu ne ya kamata kasafin kudi ya rika zuwa daga bangaren talakawa, saboda su ne suka fi sanin abubuwan da suka fi tsananin bukata. Mu kuma wakillansu sai mu sanya bukatar a cikin kasafi tare da sa musu hannu. Bangaren zartarwa ya zama aiwatarwa ne nasa.

Bangaren zartarwa na zarginku da yin cushe a kasafin kudi, shin wane dalili ya sa kuke haka?

Ni ban yarda da wannan kalma ta cushe ba. Ai yarda da ikon dan majalisa ne ya sa ake kawo kasafin kudin gabansa don tabbatar da shi. Abin da muke yi na kari ko ragi a kasafin kudi bai wuce kamar gyaran fuska ba ne. Misali a nan shi ne, kamar a Kano sai gwamnati ta sa aikin yin dakin shan magani a asibitin Murtala a cikin kasafi da ta gabatar. To a yayin gabatarwa sai dan majalisar da ke wakiltar yankin ya mike ya ce rijiyar burtsatse suka fi bukata, in ya so dakin shan magani ya biyo baya. Ko ma ya dauke aikin daga wajen dungurugum, ya ce a kai shi wani kauye a yi shi. To a nan dan majalisa ya yi aikinsa kamar yadda wadanda yake wakilta suke bukata.