Mutane sun wawushe kayan abincin da gwamnati ta killace

Mutane sun yi kukan kura sun fasa rumbun ajiyar kayan abincin gwamnatin Bayelsa suka kwashe abin da suka samu a ciki.

Mutane sun wawushe kayan abincin da gwamnati ta killace

Wani sashe na kayan abincin da Ministar Jinkai da Agajin Gaggawa, Sadiya Umar Farouk, ta mika wa gwamnatin jihar Kano. (Tsohon hoto)

Jama’ar gari sun wawushe kayan abinci da gwamnati ta killace a wanin rumbun ajiyarta tun a shekarar 2022 da nufin za ta raba domin rage radadin ibtila’in ambaliyar ruwa. 

Mutanen sun yi kukan kura ne suka fasa rumbun ajiyar hatsi da sauran kayan abincin Gwamnatin Jihar Bayelsa, suka kwashen kayan abincin da suka samu a ciki.

Sai dai Hukumar Agajin Gaggawa ta jihar (SEMA) ta sanar cewa kayayyakin abincin da aka kwashe sun riga sun lalace, kuma duk wanda ya ci zai samu matsala.

Babban daraktan hukumar, Walamam Sam Igrubia, ya ce a shirinsu na tunkarar ambaliyar ruwa a bana, shugaban hukumar ya ziyarci wurin, inda ya iske kayan abincin da suka rage, musamman shinkafa da garin rogo ba za su ciwu ba.

Wannan dai shi ne karo na biyu, bayan an Jihar Adamawa inda jama’a ke fasawa su kwashe yakan abinci daga rumbunan ajiyar kayan abinci, sakamakon tsananin tsadar kayan masarufi da ’yan Najeriya ke fama da shi.

Tun bayan cire tallafin man fetur a kasar farashinsa ke ta ninkuwa, wanda hakan ya haifar da tashin gwauron zabon kayayyaki.

A cikin wata uku da aka janye tallafin man, farashin litarsa ya ninku daga Naira 190 zuwa Naira 620.

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu