Mutanen Adamawa ba su goyon bayan dage zabe – Dokta Ardo

Al’ummar Jihar Adamawa sun yi fatali da kiraye-kirayen da ake yin a a dage zaben bana, inda suka bukaci Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi watsi da kiran da Gwamnan Jihar Mista James Bala Ngilari na ta dage zaben jihar zuwa watan Afrilu mai zuwa.  Wani fitaccen dan siyasa Dokta Umar Ardo ne ya […]

Mutanen Adamawa ba su goyon bayan dage zabe – Dokta Ardo
Mutanen Adamawa ba su goyon bayan dage zabe – Dokta Ardo

Al’ummar Jihar Adamawa sun yi fatali da kiraye-kirayen da ake yin a a dage zaben bana, inda suka bukaci Hukumar Zabe ta kasa (INEC) ta yi watsi da kiran da Gwamnan Jihar Mista James Bala Ngilari na ta dage zaben jihar zuwa watan Afrilu mai zuwa. 

Wani fitaccen dan siyasa Dokta Umar Ardo ne ya bayyana haka a martanin da ya mayar kan bukatar Gwamnan Jihar Mista James Bala Ngilari na a dage zaben inda ya ce “A doka Gwamna bai da damar daga zabe a jihar kuma ya kamata kada Hukumar INEC ta saurare shi, ta tsaya ta yi abin da ya dace.”
Dokta Ardo ya kara da cewa “A halin yanzu kowa ya shirya wa zaben bana kuma mutane da dama na jiran lokaci ne domin zaben gwarzonsu.” Ya ce Gwamna Ngilari na son a dage zaben ne ba don komai ba sai don ya ga ba zai kai labari ba a zaben.
“Ngilari ya ce a dage zaben ne don yana ganin ba zai kai labari ba. Domin ya rasa tikiti zabe na jam’iyyarsa duk da cewa yana Gwamna a yanzu. Idan za a tambaye ni ra’ayina game da hakan, zan ce ba zai ci nasara ba a wannan zaben don haka ne yake take dokokin zabe na kasar nan,” inji shi.
Ya ce, a lokacin da Ngilari ya nemi dage zaben, ya ce yana magana ne bisa abin da mutanen jiharsa suka ga ya fi cancanta, inda ya musanta haka. Ya ba zai iya tuna lokacin da Gwamnan ya kira koda mutum daya ya yi shawara da shi kan hakan a dage zaben ba.