Mutanen Buni Yadi sun bukaci a mayar da su garinsu

Mutanen garin Buni Yadi hedikwatar karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe da suke zaman gudun hijira sun nemi gwamnatin jihar da jami’an tsaro su taimaka su maida su zuwa garinsu ganin cewa zaman lafiya ya kankama a yankin.A makon jiya ne wadansu daga cikin shugabannin al’ummar garin na Buni Yadi suka kai kokensu wurinMai martaba […]

Mutanen Buni Yadi sun bukaci a mayar da su garinsu
Mutanen Buni Yadi sun bukaci a mayar da su garinsu

Mutanen garin Buni Yadi hedikwatar karamar Hukumar Gujba a Jihar Yobe da suke zaman gudun hijira sun nemi gwamnatin jihar da jami’an tsaro su taimaka su maida su zuwa garinsu ganin cewa zaman lafiya ya kankama a yankin.
A makon jiya ne wadansu daga cikin shugabannin al’ummar garin na Buni Yadi suka kai kokensu wurin
Mai martaba Mai Gujba, Mai Muktar Ibn Ali Gangaran don nuna masa bukatarsu ta a ba su damar sake komawa garinsu inda Sarkin ya mika bukatarsu ga Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam.
Aminiya ta gana da Alhaji Bukar Makinta daya daga cikin kusoshin kungiyar masu sayar da siminti a Buni Yadi inda ya ce, kusan dukan garuruwan da ke kusa da su kamar Katarko da Gujba da Buni Gari da Bularafa da Bara da sauransu mutanen garuruwan sun koma.
Ya ce, su al’ummar garin Buni Yadi, yadda suke dauka shi ne gwamnatin jihar ta ki barin su don komawa garin ne watakila saboda gwamnatin ta mayar da su abin samun kudi ta hanyar karbar taimako daga wurare da dama na gwamnati da kungiyoyin ba da tallafi na cikin gida da waje da daidaikun jama’a.
 Ya ce idan aka mayar da su gidajensu ire-iren wadannan taimako kai-tsaye za a kai musu ne maimakon a bai wa gwamnatin.
Shi ma Muhammad Tahiru Mailemo da ke gudun hijira a Damaturu cewa ya yi babban abin da ke damun su ’yan gudun hiijirar Buni Yadi shi ne amfani da ake yi da su ana karbar kudin taimako ba tare da yana isowa gare su ba, kuma jami’an karamar hukumarsu su yin biris kan kula da su inda aka mayar da su kamar mabarata.
Aminiya ta samu jin ta bakin babban jami’in soja mai kula da jihohin da ake fama da rikicin Boko Haram Birgediya Janar M.S. Aliyu ya ce, tabbas harkokin tsaro sun inganta a illahirin yankin illa matsalar ita ce hanyar motar da ta tashi daga Damaturu zuwa Buni Yadi ta zarce garin Biu a Jihar Borno ta lalace, don haka a yanzu suna kokarin matsa lamba ga gwamnatin jihar don ta gaggauta gyara ramukan da ke kan hanyar duk da cewa ta Gwamnatin Tarayya ce.
Ya tabbatar wa jama’ar garin Buni Yadi cewa, nan da ’yan makonni za su ba su izinin komawa gidajensu da zarar an gyara ramukan da ke kan hanyar musamman daga garin Gujba zuwa Buni Yadi da ruwan sama ya zagwanye ta.
A wani labarin Gwamnan Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Gaidam ya ba da tabbaci ga ’yan gudun hijirar da ke sansanonin Kasaisa da Kukareta cewa nan gaba kadan za a mayar da su garuruwansu da zarar an samu amincewar haka daga jami’an tsaro.
Gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin Mataimakinsa Injiniya Abubakar Aliyu yayin da ya ziyarci sansanonin ’yan gudin hijirar don duba halin da suke ciki.
Gwamna Gaidam ya ce, gwamnatin jihar da Gwamnatin Tarayya sun damu kan halin da suke ciki, kuma in Allah Ya yarda nan ba da jimawa ba za a maida su garuruwansu.
Ya bukaci ’yan gudin hijirar su guji karya farashin kayayyakin da ake ba su tallafi suna sayarwa maimakon yin amfani da su.