Mutanen da aka kashe a Sakkwato ma da alaƙa da Lakurawa —Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta yi zargin cewa mutanen da jirgin soji ya halaka a Jihar Sakkwato nada alaƙa da ’yan ta’addan Lakurawa.

Mutanen da aka kashe a Sakkwato ma da alaƙa da Lakurawa —Sojoji

Rundunar Sojin Najeriya ta yi zargin cewa mutanen da jirgin soji ya halaka a Jihar Sakkwato nada alaƙa da ’yan ta’addan Lakurawa.

Rundunar ta bayyana cewa Jiragenta ne suka kai harin a ci gaba da aikin fatattakar ’yan ta’adda da take yi a yankin Arewa.

Kodinetan Cibiyar Yaɗa Labarai na Rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar-Janar Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa

Rundunar Sojin Najeriya ta yi zargin cewa mutanen da jirgin soji ya halaka a Jihar Sakkwato nada alaƙa da ’yan ta’addan Lakurawa.

Rundunar ta bayyana cewa Jiragenta ne suka kai harin a ci gaba da aikin fatattakar ’yan ta’adda da take yi a yankin Arewa.

Kodinetan Cibiyar Yaɗa Labarai na Rundunar Operation Fansan Yamma, Laftanar-Janar Abubakar Abdullahi, ya bayyana cewa rundunar ba ta kai hari a yankin da take yi da Lakurawa, sai bayan ta gudanar da zuzzurfan bincike tare da tantance bayanan da ta tattara.
Ya bayyana cewa, “ya kamata mutane su sani cewa
wuraren da aka kai hare-haren a yankunan Gidan Sama da Rumtuwa an samu sahihan rahotanni da ke tabbatar da cewa suna alaƙa da Lakurawa, wannan ne ya kara bayar da ƙarfin gwiwan kai harin.”

A cewar Laftanar-Kanar Abubakar Abdullahi, ya kamata mutane su riƙa tantance sahihancin duk labarin da suka samu daga inda ya dace domin guje wa yaɗa labaran ƙarya.

“Akwai haɗarin yiwuwar ’yan ta’adda su yi ƙoƙarin yada labaran karya da nufin kawo nakasu ga aikin sojoji na murkushe su,” in ji shi.