Mutanen da aka sace a cocin Kwara sun mutu a hannun ’yan bindiga

Wanda ya tsira daga hannun maharan ne ya tabbatar da rasuwar mutane biyar.

Mutanen da aka sace a cocin Kwara sun mutu a hannun ’yan bindiga

Mutum biyar daga cikin masu ibadar da aka sace a lokacin da ’yan bindiga suka kai hari cocin ECWA da ke Omugo, a gundumar Oro Ago, Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta jihar Kwara, sun rasu a hannun maharan.

Faston cocin, Rabaran Timothy Omole ne, ya sanar da labarin ta kafar WhatsApp na cocin, sannan ya tabbatar da hakan a wata tattaunawar wayar tarho da Aminiya a daren ranar Laraba.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu matar faston ce, Misis Rachael Oluwaremilekun Omole.

Waɗannan mutane na cikin masu ibada takwas da aka yi garkuwa da su lokacin da ’yan bindiga suka kai hari cocin a ranar 22 ga watan Maris, 2026.

Rabaran Omole, ya ce wannan labari ya girgiza shi matuƙa.

Ya bayyana cewa daga cikin mutum takwas da aka sace, uku ne kawai har yanzu suke raye kuma suna hannun waɗanda suka sace su.

Ya bayyana sunayen waɗanda suka rasu; Elder Chief David Omopariola, Cif Joseph Ibitoye Afariogun, Misis Iyabo Aniyi, Elder Joshua Akanbi Adeyemi da Misis Rachael Oluwaremilekun Omole.

Faston, ya yi addu’ar Ubangiji Ya bai wa iyalansu da ɗaukacin cocin haƙurin jure wannan babban rashi.

A cewarsa, ya samu labarin ne a wajen Mista Sunday Bakare, wanda ya kasance ɗaya daga cikin wadanda aka sace.

Bakare, ya samu nasarar tserewa daga hannun masu garkuwar bayan ya shafe sama da wata guda a hannunsu.

Bakare, ya shaida wa cocin cewa mutane biyar daga cikin waɗanda aka sace sun mutu.

Majiyoyi sun ce wasu daga cikin waɗanda aka sace na fama da rashin lafiya kuma suna shan magunguna, amma an hana su samun magungunansu a lokacin da suke tsare.

An kuma ruwaito cewa an sanar da iyalan waɗanda abin ya shafa game da mutuwarsu, amma har yanzu ba a san takamaiman dalilin mutuwar ba.

Bayan sace mutanen, maharan sun nemi kuɗin fansa Naira biliyan ɗaya.

Daga baya suka rage kuɗin zuwa Naira miliyan 150.

Majiyoyi sun ce iyalan waɗanda aka sace sun tara kusan Naira miliyan 20 tare da kayan abinci da wasu kayayyaki da maharan suka buƙata kafin sako mutanen.

Sai dai duk da karɓar kuɗin da kayan, maharan sun ƙi sakin waɗanda suka sace.

Har yanzu ana kyautata zaton cewa mutane uku daga cikin waɗanda aka sace na nan a hannun masu garkuwa da mutanen.