Mutanen da aka yi yunkuri fataucinsu sun shiga hannu a Katsina

Hukumar Shigi da Fici a Jihar Katsina ta gabatar da mutum 12 cikinsu har da kananan yara biyu ’yan shekara 9 da 11 da aka yi yunkurin yin fataucinsu ta hanyar tsallakewa da su Jamhuriyar Nijar. A lokacin da yake gabatar da mutanen da suka hada da maza hudu mata takwas, shugaban hukumar Mohammed Alhaji […]

Mutanen da aka yi yunkuri fataucinsu sun shiga hannu a Katsina
Mutanen da aka yi yunkuri fataucinsu sun shiga hannu a Katsina

Hukumar Shigi da Fici a Jihar Katsina ta gabatar da mutum 12 cikinsu har da kananan yara biyu ’yan shekara 9 da 11 da aka yi yunkurin yin fataucinsu ta hanyar tsallakewa da su Jamhuriyar Nijar.
A lokacin da yake gabatar da mutanen da suka hada da maza hudu mata takwas, shugaban hukumar Mohammed Alhaji Alfa, ya ce, jami’ansu da ke sintiri a kan iyakar Kongolam ne suka kama mutanen da ke yunkurin tsallakawa ta garin Maimujiya zuwa cikin Nijar inda suke bi ta Agadas har zuwa kasar Libiya. “Dukkansu babu wanda ya mallaki wata takardar shaidar yin zirga-zirga a tsakanin kasa da kasa,” inji shi. Ya ce, fataken mutanen sun yaudare su ne da sunan nema musu aiki a kasashen waje ta hanyar shiga da su ta barauniyar hanya. Ya ce, wadannan fataken da ke gudanar da aika-aikarsu daga Jihar Kano suna amfani da kan iyakoki ne domin aiwatar da muguwar dabi’arsu. “Har yanzu muna neman direban motar da muke zargi shi ne jagoran da zai fita da mutanen da suka fito daga jihohin Edo da Delta, wanda ya tsere a lokacin da muka rutsa da su.”
Mutanan da aka kama sun hada da Precious Christoper mai shekara 38, sai Faith Sazuwa mai shekara 26 da Glory Igbinadour mai shekara 21 da Oghoghi Kelly mai shekara 22 dukkansu daga Jihar Edo. Sauran sun hada da Joy Obi mai shekara 35 da Peter Enerine mai shekara 27 da Jasper James mai shekara 29, da Lucky Odion mai shekara29 da Ejiro Ereghare mai shekara 34 sai Meyer Obi mai shekara tara da Gift Obi mai shekara 11. Tuni hukumar ta iza keyarsu zuwa ofishin shiyya na Hukumar Yaki da Fataucin Mutane (NAPTIP) da ke Kano don ci gaba da bincike tare da daukar mataki na gaba.