Mutanen da ba za a kara wa kudin lantarki ba

Hukumar kula da watar lantarki (NERC) ta ce mutane da ba su samun wutar lantarki ta akalla awa 12 a raba ba za cikin wadanda za a yi wa karin kudi. Ta ce kamfanonin raba wutar (Discos) ba su isa su kara kudi ba sai sun tattauna da masu amfani da ita, sun kuma rika […]

Mutanen da ba za a kara wa kudin lantarki ba

Turakun wutar lantarki

Hukumar kula da watar lantarki (NERC) ta ce mutane da ba su samun wutar lantarki ta akalla awa 12 a raba ba za cikin wadanda za a yi wa karin kudi.

Ta ce kamfanonin raba wutar (Discos) ba su isa su kara kudi ba sai sun tattauna da masu amfani da ita, sun kuma rika samar da ita na akalla awa 12 duk rana.

Shugaban Hukumar, Farfesa James Momoh, ya ce, “Duk ma yadda aka yi, karin ba zai shafi talakan Najeriya ba. A dalilin haka ya sa aka ce DisCos su tattauna da masu amfani da wutar bisa tsarin adadin wutar da ka sha”, inji Momoh

NERC ta kuma shardanta wa da Discos tattaunawa da masu amfani da wutar, tabbacin yawan wutar da za su rika bayarwa; sanya mita a makarantu; da kuma daina kintacen kudin wuta fiye da kima.

Sa’annan karin ba zai shafi masu amfani da wutar da bata wuce 50 kilowatts ba, da kuma wadanda ba su samun wutar da bata kai awa 12 a rana ba.

“Karkashin wannan tsarin na adadin wutar da aka sha, Discos za su iya kara kudin wutar ne kawai idan suka kara yawan awannin da ingancin watar da suke bayarwa a kullum”, inji Momoh.

Sai dai ba a bayyana ranar da Discos za su kara kudin wutar ba, amma an amince musu fara tuntubar masu amfani da wutar da bin sauran hanyoyin karin.

Aminiya ta ji cewar kamfanonin raba wutar lantarki uku sun gabatar wa NERC canje-canjen da suka yi na tsarin inganta wutar da zai ba su damar kara kudin wutar.

Ana hasashen karin da kamfanonin suka so yi a watan Yuli zai kai kashi 47 cikin dari, amma Majalisar Tarayya ta taka musu birki.