Mutanen da Buhari ya aminta da su ke yaudarar shi —Solomon Dalung
Tsohon ministan ya ce mutanen da Buhari ya aminta da su ke jawo mishi zagi.
Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya ce gazawar gwamnatin Shugaba Buhari ta samo asali ne daga gazawar mutanen da ya aminta da su, wadanda ke ta jawo mishi matsala da ’yan Najeriya.
Dalung, ya ce babu abin da zai wanke Buhari daga abin da jami’an gwamnatinsa ke yi saboda shi ne shugaba, don haka ya shawarce shi da ya yi duk abin da ya dace a kan lokaci domin dawo da kimarsa a idon duniya.
- Ya kamata ’yan siyasa su rika zaman gidan yari —Sanata Ndume
- ’Yan kwallon Najeriya 3 da ke daukar sama da miliyan 30 a sati
Ya wallafa a shafinsa na Facebook cewa, mutuncin Buhari kadai ba zai wadatar ba wajen daidaitar al’amura a Najeriya, muddin shugaban ya nada mutanen da aikinsu ya saba da abin da aka san shi a da kuma manufofinsa.
“Da kowannensu yana yin aikinsa yadda ya kamata da jama’a ba za su yi wadannan surutan ba game da gazawar gwamnatinmu.
“Kai ka dogara da su wajen gudanar da gwamnati, kana kuma gaskata abin da suke fada maka, amma kuma su ba gaskiyar yadda abubuke suke tafiya suke bayyana maka ba.
“Nauyin shugabanci ya sa ka a gaba don haka kama bukatar masu taimaka maka, amma sai aka yi rashin dace, duk da kyawawan manufofinka, mutane da ke zagaye da kai fadi-tashinsu kawai suke yi na cim-ma abubuwan da suka saba wa nauyin da ya rataya a wuyanka,” kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Solomin Dalung ya yi minista a wa’adin mulkin Buhari na farko daga 2015 zuwa 2019, kuma ya yi fice a tsawon lokaci wurin kare Shugaba Buhari da gwamnatinsa.