Mutanen da cutar Coronavirus ta harba a Najeriya sun zarta dubu 58

A yanzu watanni bakwai kenan da bullar cutar coronavirus a Najeriya bayan bullarta karon farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020. Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC) ta saba fitarwa duk rana, sun nuna cewa daga farkon bullar cutar a kasar zuwa yanzu, mutum 58,324 ne suka harbu. Babu […]

Mutanen da cutar Coronavirus ta harba a Najeriya sun zarta dubu 58

Wani jami’in kiwon lafiya yana daukar samfur a daya daga cikin cibiyoyin da aka kafa da taimakon NCDC a wasu al’ummun Yankin Babban Birnin Tarayya

A yanzu watanni bakwai kenan da bullar cutar coronavirus a Najeriya bayan bullarta karon farko a ranar 27 ga watan Fabrairun 2020.

Alkaluman da Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya (NCDC) ta saba fitarwa duk rana, sun nuna cewa daga farkon bullar cutar a kasar zuwa yanzu, mutum 58,324 ne suka harbu.

Bayanan NCDC sun nuna cewa mutum 49,794 ne suka warke daga cutar bayan kamuwa, yayin da mutum 1,108 suka riga mu gidan gaskiya.

Kididdigar da Hukumar ta fitar a ranar Lahadi, 27 ga watan Satumban 2020, ya nuna cewa mutum 7,422 suka rage masu dauke da kwayoyin cutar a fadin kasar.

Ga kididdigar alkaluman da NCDC ta fitar kan cutar da wadanda suka mutu a kowacce daga cikin jihohi 36 na kasar da kuma birnin Abuja:

Jihohi Kamuwa Mutuwa
Legas 19,239 205
Abuja 5,674 77
Oyo 3,254 39
Edo 2,624 107
Filato 3,388 33
Ribas 2,347 59
Kaduna 2,397 38
Kano 1,737 54
Delta 1,802 49
Ogun 1,836 28
Ondo 1,631 36
Inugu 1,289 21
Ebonyi 1,040 30
Kwara 1,032 25
Katsina 857 24
Osun 827 17
Abiya 891 8
Borno 741 36
Gombe 864 25
Bauchi 698 14
Imo 568 12
Binuwai 481 10
Nasarawa 449 13
Bayelsa 398 21
Jigawa 325 11
Akwa Ibom 288 8
Neja 259 12
Ekiti 321 6
Adamawa 234 16
Anambra 237 19
Sakkwato 162 17
Kebbi 93 8
Taraba 95 6
Kuros Riba 87 9
Zamfara 78 5
Yobe 76 8
Kogi 5 2