Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

Akasarin waɗanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar ɗiban man da ya zube bayan motar ta kife.

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

Kawo yanzu adadin waɗanda suka rasu sakamakon fashewar tankar man fetur da ta auku ranar Asabar a Jihar Neja sun kai 86 kamar yadda mahukunta suka tabbatar.

Wannan na ƙunshe cikin alƙaluman waɗanda lamarin ya shafa da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja ta fitar yau Asabar.

Da yake yi wa manema labarai jawabi, shugaban hukumar, Abdullahi Baba Arah, ya ce zuwa yanzu sun tattara gawawwaki 86 yayin da wasu 55 ke kwance a yanayin na ban tausayi.

Baba Arah ya ce tuni sun binne gawawwaki 80 yayin da suka miƙa wasu biyar zuwa ga ’yan uwansu domin yi musu tasu jana’izar a gida.

Sai dai ya ce bayan kammala binne gawawwakin, ɗaya daga cikin waɗanda ke kwance a cibiyoyin kiwon lafiyar da aka kai waɗanda abin ya shafa shi ma ya ce ga garinku nan.

Bayanai sun ce ana jinyar waɗanda abin ya shafa a Babban Asibitin Sabon Wuse da Suleja da kuma Cibiyar Lafiya da ke Dikko.

Aminiya ta ruwaito gomman mutane sun mutu yayin da wasu da dama suka jikkata bayan da wata motar dakon mai ta kife, ta kuma zubar da mai da kafin daga bisani ta fashe a Jihar Neja.

Lamarin kamar yadda rahotanni suka tabbatar ya faru ne a kusa da Dikko Junction da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a wanda ke Ƙaramar Hukumar Gurara ta Jihar Neja.

A cewar Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) shiyyar Neja, Kumar Tsukwam, akasarin waɗanda abin ya rutsa da su talakawa ne mazauna yankin da suka yi gaggawar ɗiban man da ya zube bayan motar ta kife.

“Mutane da yawa sun taru domin ɗiban mai duk da ƙoƙarin da aka yi na hana su,” inji Tsukwam a cikin wata sanarwa.”

Gwamnan Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa a sanarwar da sakataren watsa labaransa, Bologi Ibrahim ya fitar.

Ana iya tuna cewa, a watan Oktoban shekara 2024 da ta gabata aƙalla mutum 140 ne suka mutu sakamamon konewar da suka yi lokacin da wata babbar motar ɗaukan mai ta kama da wuta a Jihar Jigawa.

Sojoji sun kashe ɗan Bello Turji

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki a Gaza

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja