‘Mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu sun haura miliyan 2’

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa adadin zai iya karuwa a kan haka.

‘Mutanen da rikicin Ukraine ya raba da muhallansu sun haura miliyan 2’

Yadda mutane suke ficewa daga Ukraine

Shugaban Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), Filippo Grandi, ya ce akalla mutum miliyan biyu ne suka bar Ukraine don neman mafaka a wasu kasashen tun bayan fara yaki a kasar.

Ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce ana sa ran adadin ya karu yayda Rasha ke ci gaba da luguden wuta a kan kasar Ukraine.

Hukumar ta kuma yi gargadin cewa zagaye na biyu na ’yan gudun hijirar zai iya ninka wanda ake gani yanzu.

Wani jami’in kula da kan iyakar kasar Poland ya ce akalla mutum miliyan daya da dubu 200 ne suka tsallaka kasarsu daga Ukraine tun bayan fara yakin.

A wani labarin kuma, daruruwan mutane ne ke ta tururuwar barin biranen Sumy da Irpin da ke dab da babban birnin kasar na Kyiv, bayan Rasha ta sanar da tsagaita wuta domin mutanen su samu damar ficewa.

Matakin na zuwa ne bayan hukumomin Rasha sun sanar da bayar da kafar ficewa ga fararen hula daga biranen da dakarun Rashar suka mamaye.

Gwamnan yankin Kyiv, Oleksiy Kuleba, ya ce ya zuwa karfe 9:30 na safiyar ranar Talata, sama da mutum 150 ne aka kwashe daga birnin.