Mutanen da suka mutu a harin wuta a masallacin Kano sun karu zuwa 23

Mutum biyu sun tsira daga cikin mutanen da matashin ya cinna wa wuta suna jam’in sallar asuba a masallaci

Mutanen da suka mutu a harin wuta a masallacin Kano sun karu zuwa 23

Adadin mutanen da suka mutu bayan wutar da aka cimma musu a cikin masallaci a Jihar Kano ya karu zuwa 23.

Kawo yanzu dai mutum biyu ne suka tsira cikin masallata da harin ya rutsa da sun a yayin da suke Sallar Asuba.

Mutanen jam’in sallar asuba a lokacin da wani matsahi mai shekaru 38, ya cinna musu wuta a garin Larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar.

Aminiya ta kai ziyara inda aka kwantar da 24 daga cikinsu a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano, inda muka gano 22 sun rasu, ragowar biyu suna raye.

Na 25 dinsu da ke kwance a Asibitin Koyarwa na Malam Aminu Kano kuma ya rasu.

Jami’an asibiti sun bayyana cewa an sallami daya daga cikin ragowar marasa lafiyan daya kuma yana murmurewa.

Aminiya ta ruwaito cewa, wanda ake zargi ya watsa man fetur a masallacin, ya kulle kofa, sannan ya banka wuta a lokacin da mutane sama da 30 suke sallar asuba a ciki.

An gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun shari’a da ke karkashin jagorancin Halhalatu Zakariyya tare da tsare shi a gidan yari.

Matatar Warri ta fara aiki bayan shekara 9

’Yan sara-suka sun yi wa tela kisan gilla a Jos

Bakanuwa ta zama ’yar Arewa ta farko da ta zama Kwamishinan ’yan sanda

Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin dubin watan Rajab