Mutanen da ya kamata su zama shugabannin majalisa

Kamar yadda a kullum muke fadin cewa mafi yawan wadanda muka zaba a matsayin sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai rigar Baba Buhari suka shiga, wannan magana tabbas haka take. A bisa wannan dalili ne ma muke ganin cewa ai Baba Buhari duk wani abu da ya sa a gaba zai yi shi, cikin ruwan sanyi […]

Mutanen da ya kamata su zama shugabannin majalisa
Mutanen da ya kamata su zama shugabannin majalisa

Kamar yadda a kullum muke fadin cewa mafi yawan wadanda muka zaba a matsayin sanatoci da ’yan Majalisar Wakilai rigar Baba Buhari suka shiga, wannan magana tabbas haka take. A bisa wannan dalili ne ma muke ganin cewa ai Baba Buhari duk wani abu da ya sa a gaba zai yi shi, cikin ruwan sanyi a kasar nan amma ina sai muka ga lissafi ya juya. Hasali ma wadansu daga cikin irin wadannan mutane da muke ganin za su yi aiki da Baba Buhari kafada-da-kafada wajen gina kasarmu sun bangare ne tare da kafa wata runduna domin tarwatsa shirin Baba Buhari na gyara kasarmu, wato a boye suna yi wa wasu iyayen gidansu aiki.

Abin da muka so a ce wakilanmu sun yi mana shi ne su yi aiki da Baba Buhari kut-da-kut, duk abin da zai yi suna rawar jiki su amince kuma su ba shi karfin gwiwa, kai wani abin ma idan ya fadi suka ga ya yi buris su ce, da shi maigida ka ce za a yi abu kaza ko kuma mun fuskanci kana son a yi abu kaza amma ka ki gabatar mana da kudirin? Irin haka muka so a ce zaurukan majalisunmu sun zama a mulkin Baba Buhari.

Amma abin sai ya zo mana da ba-zata. Da a ce wakilan n majalissunmu sun zama masu tsantsar biyayya ga Baba Buhari tsawon shekara daya zuwa biyu kuma muka ga lamuran kasar ba su daidaita ba to da mu da kanmu talakawa za mu fara fadin ya kamata a daina yi wa Baba Buharin nan biyayya tunda an bi tasa kasar ta kasa daidaita, amma ina! Wakilan majalisarmu sai suka fandare a tashin farko suka fara gaban kansu. Kun ga dole ko da Baba Buhari ya yi wani abu da bai dace ba mu kasa ganin laifinsa sai naku.

Sabuwar majalssa a yanzu muna fatan za ta zama mai tsantsar biyayya ga Baba Bahari. In a ce akwai wata alfarma da zan nema a wurin ’yan majalisar bai wuce ta su bi Baba Bahuri sau da kafa ba. Idan kuka zama haka kun gama yi wa talaka komai kuma mu da kanmu za mu yi wa Baba Buhuri hukunci mai kyau idan adalcinsa ya bayyana, haka zalika ba fata muke ba, mu ne za mu yi masa hukunci mummuna idan kasarmu lamura suka dagule.

Baba Buhari mutum ne mai kawaici, da tsantsar bin doka a bisa wannan ne nake ganin cewa ba yadda za a yi ya nuna wani kai- tsaye ko wadansu ya ce, su yake bukatar su zama jagorori a majalisa. To amma tunda uwar jam’iyya ta shiga lamarin muna fatan za ta yi da gaske wajen ganin ba a maimaita mana irin ta baya ba. Ya Allah Ka kara wa Baba Buhari lafiya Ka ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa na shugabancin kasarmu, Ka karo mana zaman lafiya da wadatar arziki a kasarmu da ma Afirka baki daya.

Daga Nasiru Kainuwa Hadeja (Masoyin Baba Bahuri) 08100229688/09073801967.