Mutanen da ya kamata suna gidan yari Buhari ya bai wa lambar girmamawa —Buba Galadima

Buba Galadima ya ce mutum bakwai ne kawai suka cancanci lambar girmamawar, sauran ya kamata a ce suna tsare a kurkuku.

Mutanen da ya kamata suna gidan yari Buhari ya bai wa lambar girmamawa —Buba Galadima

Buba Galadima

Tsohon dan-a-mutun Shugabn Buhari, Buba Galadima, ya ce duk mutanen da shugaban ya bai wa lambar girmamawa ta kasa a bana ya kamata suna gidan yari, in banda mutum bakwai.

Buba Galadima ya yi wannan batun ne a yayin da yake magana kan lambobin girmamawa na kasa da Buhari ya bai wa mutum 447 a makon jiya, a lokacin hirar da kafar talabijin ta Arise ta yi da shi.

Ya ce, “A mutum 447 da aka bai wa lambar girmamawa ta kasa, 440 daga cikinsu ya kamata a ce suna tsare a gidan yari, maimakon gabatar da su a matsayin wadanda za abai wa lambar girmamawa.”

Cikin mutanen da aka karrama da lambobin GCON, CON, OON, MON da MFR, har da wadanda suka rasu da fitattun malaman addini.

Sauran sun hada da manyan saraukuna da attajirai da dai daidaikun mutanen da suka yi abin yabo. Akwai kuma ’yan boko da kwararru da ’yan majalisun dokoki masu ci da tsofaffi.

Buba Galadima ya ce, “Da wane dalili za a karrama su? Me suka yi da suka cancanci karramawa? An dai yi wa yaran gida ne sakayyar hidimar da suka yi.

“Shi kansa Buhari ya sha zargin tsohon Shugaba Obasanjo da marigayi Umaru Yar’Adua da Goodluck Jonathan cewa sun akwai alamar tambaya a kan dabi’un mutanen da suka bai wa lambar yabo.

“Amma a cikin mutanen da ya bai wa lambar girmamawa ta kasa, su wane ne masu nagarta?

“Da ni ne, mutanen da suka yi ritaya daga aiki ba tare da zargi a kansu ba su zan bai wa, maimakon wadanda EFCC da ICPC ke bibiyar su.

“Gara na bai wa wadanda suka rasa rayukansa wajen bauta wa kasa; Gara na bai wa kukun da na san ya iya dafa abinci sosai da in dauka ai bai wa mai sayar da katin waya wanda a dare daya ya mallaki tiriliyoyi, a ra’ayina.”