Mutanen gari sun fatattaki ’yan bindiga tare da kashe 4 daga cikinsu a Katsina

Mutanen garin sun nuna juriya ta hanyar yin artabu da maharan da suka kai wa ƙauyensu hari.

Mutanen gari sun fatattaki ’yan bindiga tare da kashe 4 daga cikinsu a Katsina

Mazauna ƙauyen Dansarai da ke Ƙaramar Hukumar Malumfashi a Jihar Katsina, sun yi artabu da ’yan bindigar da suka kai musu hari a ranar Talata, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa.

A cewar mazauna yankin, ’yan bindigar sun shiga ƙauyen ne a kan babura ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47, inda suka riƙa harbe-harbe kan mai uwa da wabi.

Mutum huɗu sun mutu nan take sakamakon harin.

Wani ganau, ya ce maharan sun fara harbi tun kafin su shiga ƙauyen, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu.

Bayan kai harin, mazauna ƙauyen tare da ’yan sa-kai sun haɗa kai inda suka tunkari ’yan bindigar.

A yayin fafatawar, an kashe ’yan bindiga huɗu, yayin da sauran suka tsere.

Wani mazaunin yankin ya ce maharan sun kasa sace dabbobi ko kwasar kayayyaki saboda juriyar da al’umma suka nuna.

A gefe guda kuma, mutum takwas sun jikkata a yayin harin.

Wasu majiyoyi sun ce wasu sun samu raunukan harbin bindiga, yayin da wasu suka ji rauni a lokacin da ake artabun, amma suna asibiti inda likitoci ke kula da su.

Mazauna yankin sun kuma zargi jami’an tsaro da gaza kai ɗauki duk da yawan kiran neman agajin da suka yi yayin harin.

Wani jagoran al’umma ya ce sun yi ta neman taimako, amma babu jami’an tsaro da suka kai musu ɗauki kafin ’yan bindigar su tsere.

Bayan aukuwar lamarin, mazauna Dansarai da maƙwabtan ƙauyukan sun roƙi Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Katsina su tura ƙarin jami’an tsaro zuwa gabashin Ƙaramar Hukumar Malumfashi, saboda yawaitar hare-haren ’yan bindiga.

Gabashin Malumfashi na daga cikin yankunan da suka fi fama da matsalar ’yan bindiga a shiyyar Funtua a Jihar Katsina.

Da aka tuntuɓi kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Katsina, Sadiq Aliyu, ya ce zai binciki lamarin kafin ya yi bayani.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba.