Mutanen gari sun kama mai garkuwa da mutane a Jos

Al’ummar yankin Nepa da ke garin Jos sun yi kukan kura sun kama mai garkuwa da mutane a ranar Alhamis, suka mika shi ga ’yan banga.

Mutanen gari sun kama mai garkuwa da mutane a Jos

Jama’ar gari a sun kama wani mai garkuwa da mutane bayan ya karbi kudin fansa Naira miliyan 1.5 a gari Jos, Jihar Filato.

Al’ummar yankin Nepa da ke garin Jos sun yi kukan kura sun kama mai garkuwa da mutanen ne a ranar Alhamis, suka mika shi ga ’yan banga.

Wani dan banga a yankin da ya nemi a boye sunansa, ya ce ’yan banga sun mika wanda ake zargin ga ofishin ’yan sanda na Laranto.

Dan bangan ya ce wanda ake zargin, “ya yi garkuwa ne da wasu kananan yara biyu, ya karbi kudin fansa Naira miliyan 1.5 daga iyayensu, amma ya ci gaba da rike yaran.

“Washegari da ya je wani kango da ya boye yaran ne mutanen da ke wucewa a wurin suka ji kukan yara, shi ne suka shiga ciki.

“Da shigarsu sai wanda ake zargin ya haura taga ya tsere, suka bi shi suka yi masa ihu, mutane suka fito maza da mata aka kama shi.

“Daga nan suka mika shi a hannun ’yan banga, su kuma suka kai shi ofishin yan sanda na Laranto tare da tsabar kudi N1,492,000 da ya riga ya karba daga iyayen yaran.”

Kakakin ’yan sanda na Jihar Filato, DSP Alabor Alfred, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a halin yanzu wanda ake zargin yana hannun rundundar tana gudanar da bincike a kansa.