Mutanen gari sun yi wa mahaukaciya kisan gilla
Daga jin rade-rade suka kama ta suka cinna mata wuta ta kone kurmus.
Wata sananniyar mahaukaciya ta gamu da ajalinta bayan mutanen unguwa sun yi mata dirar mikiya suka kona ta kurmus.
Aminiya ta kawo rahoton yadda mutane a Badagry a Jihar Legas, suka yi wa matar kisan gilla bisa rade-radin da aka yada cewa an ga ta da bindigogi hudu kirar AK-47 da sassan jikin dan Adam.
Daga nan wasu mutanen unguwar ta Abule-Ado suka yi wa mahaukaciyar da ke zama a karkashi wata gada kamun kazar kuku suka cinna mata wuta ta kone kurmus.
Sun yi ta zargin cewa badda kama take yi a matsayi mahaukaciya, tana yi wa ’yan fashi ajiyar makamai.
Amma Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas ta bayyana cewa “Muna fada da babbar murya cewa kisan gilla aka yi wa matar kawai don cimma manufar wadanda suka aikata kisan, amma babu wata hujja.”
“Bincike ya nuna cewa babu wata bindiga kirar AK-47 ko wani da da aka samu tare da ita, ko aka gano a wurin da take.
“Kashe ta kawai suka yi ba bisa hakki ba,” inji sanarwar da kakakin Rundunar, Olamuyiwa Adejobi ya fitar.
Ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Hakeem Odumosu ya ba da umarni “a gudanar da cikakken bincike a kamo sannan a hukunta wadanda ke da hannu a aikata kisan”.
Olamuyiwa Adejobi ya ce Kwamishinan ya ce ba zai lamunci duk wani nau’in daukar doka a hannu ba daga wani mutum ko wata kungiya.
A ranar Litinin da aka kashe matar, wani matashi da ke zaune a daura da unguwar, Abdullahi Alkanawiy, ya shaida wa Aminiya cewa ya zo wucewa ta wajen a mota sai ya tarar an banka wa matar wuta.
Ya ce, “Duk wanda yake wucewa ta wajen zai rika ganin ta a karkashin gada, kuma da ka gan ta ka ga mahaukaciya.”