Mutanen Geidam da suka yi gudun hijira sun samu tallafi a Gashua
Wata kungiyar ci gaban Matasa a Jihar Yobe mai suna Yobe Youth Initiative and Community Development (YOYICOD), ta taimakawa al’ummar garin Geidam da suka yi hijira zuwa Gashua bayan mamayar da mayakan Boko Haram suka kai wa garin tsawon kwanaki hudu da suka gabata. Kungiyar Matasan da ke da ofishinta a garin Gashua na Jihar […]
Yadda mutanen garin Geidam ke gudun hijira
Wata kungiyar ci gaban Matasa a Jihar Yobe mai suna Yobe Youth Initiative and Community Development (YOYICOD), ta taimakawa al’ummar garin Geidam da suka yi hijira zuwa Gashua bayan mamayar da mayakan Boko Haram suka kai wa garin tsawon kwanaki hudu da suka gabata.
Kungiyar Matasan da ke da ofishinta a garin Gashua na Jihar Yobe tare da hadin gwiwar Alhaji Adamu Alhassan (Dan Gata), sun ba da agajin gaggawa ga mazauna garin Geidan da suka yi hijira zuwa Gashua.
- Dan Majalisa ya raba wa al’ummar mazabarsa Naira miliyan 50 a Suleja
- Surutai ba za su sa mu tattauna da ’yan bindiga ba —El-Rufai
Shugaban kungiyar, Ibrahim Sunusi, ya ce sun dora ne a kan irin kokarin da gwamnatin Jihar Yobe ta Mai Mala Buni ke yi na taimaka wa ’yan gudun hijira da sauran mabukata.
Ya kuma ce Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar SEMA, ta umurci duk kungiyoyi da su fito wajen ganin sun taimaki al’ummar garin Geidam da suke shigowa ba tare da sanin inda za su tsugunna ba.
A cewarsa, ganin yadda Gwamnatin Jihar Yobe ke yi a karkashin hukumar SEMA wajen ba da agajin gaggawa, ya sanya ba za a bar su a baya ba wajen ganin an taimaka wa ’yan gudun hijran ko da da dan abun da bai taka kara ba, domin yana daga cikin akidun da ya sa suka kafa kungiyar.
Kazalika, Ibrahim Sunusi ya yi Godiya ga Allah da ya hada su da mutane a cikin kungiyarsu masu zuciyar fidda kudinsu don ganin sun taimaka mata na cimma kudirinta wajen taimakon mabukata.
Aminiya ta ruwaito cewa daga cikin kayayyakin tallafin da aka bayar sun hada da taliya da ruwa da sauran nau’ikan abinci.