Mutanen Kala Balge sun kashe dimbin ’yan Boko Haram
Mazauna garin Rann hedkwatar karamar Hukumar Kala Balge da ke Jihar Borno, sun fafata da wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne da suka kai musu hari a ranar Talatar da ta gabata, inda suka kashe da dama daga cikinsu.Mahara da dama sun je garin Rann da wajen karfe 4:00 na Asuba, inda […]

Mazauna garin Rann hedkwatar karamar Hukumar Kala Balge da ke Jihar Borno, sun fafata da wasu da ake zargin ’yan kungiyar Boko Haram ne da suka kai musu hari a ranar Talatar da ta gabata, inda suka kashe da dama daga cikinsu.
Mahara da dama sun je garin Rann da wajen karfe 4:00 na Asuba, inda suka hadu turjiya daga jama’ar garin wadanda suka samu bayanin shirin kai musu hari.
Wannan ne karo na biyu da ’yan Boko Haram suka kai hari garin Rann, sai dai a harin farko ba su shiga garin ba, yayin da a wannan karo suka samu nasarar kutsawa suka fara kashe mutane da kone gidaje kafin mutanen garin su ci karfinsu.
Wani dan majalisar jihar daga yankin ya tabbatar da kai harin inda ya ce jama’ar garin sun samu nasarar murkushe harin. “Mutanen kauyen sun samu nasarar kare kauyensu. Sun kashe ’yan kungiyar da dama, wasu kuma sun gudu da miyagun raunuka,” inji shi. Ya kara da cewa, “Mutanenmu sun kwato babura 70 da maharan suka zo da su, kuma sun kwato motoci kirar Hilud biyu da motar yaki (APC) daya, yayin da aka kama wasu maharan da ransu.”
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Borno Lawan Tanko ya ce bai da masaniya kan harin. “Labarin da kawai na samu an ga maharan a wuraren hanar Hamchika zuwa Kala Balge. Kuma mun sanar da sauran hukumomin tsaro halin da ake ciki,” inji shi.
Gidan rediyon BBC Landan ya ce, samarin garin da ke taimaka wa jami’an tsaro da wasu dakaru sun yi wa maharan kwanton bauna, inda suka kashe ’yan Boko Haram kusan 200 wasu kuma suka samu raunuka.
A makon jiya ne ’yan Boko Haram suka kai hari Gamboru Ngala makwabciyar Kala Balge, inda suka kashe sama da mutum 400 da lalata motoci sama da 300 da babura 650 da gine-ginen gidajen jama’a da na gwamnati da babbar kasuwar garin.