Mutanen Kano sun yi wasa da annoba ta bi gari —El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i yace al’ummar jihar Kano sun yi wasa da annobar coronavirus ta kuma bi gari don haka ba zai bari su shigo da ita Kaduna ba. Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wani fefen bidiyo a sa’ilin da yake ganawa da muqaraban gwamnatin sa a baya bayan nan, inda  […]

Mutanen Kano sun yi wasa da annoba ta bi gari —El-Rufa’i

Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i yace al’ummar jihar Kano sun yi wasa da annobar coronavirus ta kuma bi gari don haka ba zai bari su shigo da ita Kaduna ba.

Gwamna El-Rufa’i ya bayyana haka ne a wani fefen bidiyo a sa’ilin da yake ganawa da muqaraban gwamnatin sa a baya bayan nan, inda  yasha alwashin fita ranar salla ya kuma datse hanyar da ta hade jihar Kano da Kaduna domin ya tabbatar babu wanda ya shigo saboda gudun kada a yada cutar annobar coronavirus daga jihar Kano zuwa  Kaduna.

” Duk ma mai wani shirin zuwa daga Kano ya sani ina nan ina jiran shi, kuma ba zan bar wurin ba sai dare yayi.

” Domin dole ne mu hana mutane wadanda su sun yi wasa da wannan ciwo, yabi gari yayi kanta kuma su kawo mana shi.

” Dole ne mu kare al’umar mu, abin da muke yi ke nan, mutane da yawa ba zasu ji dadi ba” in ji Nasiru El-Rufa’i

Yace da kansa zai fita  rana sallah, ya je hanyar Kano domin ya ga wanda  zai shigo Kaduna a  ranar.

” Kuma ni ran salla zanje hanyar Kano inga wanda zai shigo Kaduna ranar, ni da kai na zanje”

A lokacin da Gwamna Nasiru El-Rufa’i na jihar Kaduna ke  daukar  wannan mataki a makwabciyar jihar,  takwaran sa na Kano Abdullahi umar Ganduje ya baiwa alummar jihar daman su fita sallar Idi bisa sharadin kiyaye matakan kariyar daga annobar coronavirus, tare da sharadin ba za a yi shagugulan sallah da suka hadarda hawan sallah a daukacin masarautun biyar na jihar.