Mutanen kauyen Jaruwa sun yi wasan kura da barawon awaki

Wani da ake zargin barawon awaki ne ya sha kashi a hannun mutanen kauyen Jaruwa da ke karamar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa har sai da ya suma bayan da aka zarge shi da satar awakin wani mai suna Suleiman Adamu a ranar Litinin da ta gabata.barawon mai kimanin shekara 35 mai suna Yusuf Musa […]

Mutanen kauyen Jaruwa sun yi wasan kura da barawon awaki
Mutanen kauyen Jaruwa sun yi wasan kura da barawon awaki

Wani da ake zargin barawon awaki ne ya sha kashi a hannun mutanen kauyen Jaruwa da ke karamar Hukumar Jahun ta Jihar Jigawa har sai da ya suma bayan da aka zarge shi da satar awakin wani mai suna Suleiman Adamu a ranar Litinin da ta gabata.
barawon mai kimanin shekara 35 mai suna Yusuf Musa haifaffen karamar Hukumar Kiyawa an mika shi ga jami’an hukumar tsaro ta farin kaya ta cibil defense a ranar Litinin, bayan mutanen kauyen sun kama shi yana kokarin tserewa da wasu awaki 11 da ya sata.
Jami’an hukumar tsaron sun shaida wa wakilimmu cewa ana zargin Yusuf ya jima yana satar dabbobin jama’a, amma bai taba fadawa hannun hukuma ba.
Shugaban hukumar cibil defence a jihar Muhammed Gidado ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin ya shaida masa cewa ya yi shigar matafiyi ne da wasu jakunansa uku ya yi tattaki zuwa kauyen Jaruwa domin nazarin inda zai saci awakin.
Ya ce wata dabara ta fado masa inda ya yi sallama da wani magidanci mai suna Sulaiman Adamu ya nemi ya taimaka masa da wurin kwana, kuma da ya taimaka masa a matsayin matafiyin da dare ya yi masa. Ya ce da gari ya waye sai maigidan ya yi masa rakiya, ya ce ashe cikin dare ya sace masa awaki a bayan gida ya kai su cikin wata sarkakiya nesa da gari ya boye.
Ya ce bayan maigidan ya dawo ne sai hankalinsa ya koma kan awakinsa inda ya ga ba su nan, sai ya sanar da makwabta suka bazu bayan gari neman dabbobi, can sai aka hangi Yusif yana kokarin tserewa da su.
Ya ce jakunansa suna hannun Adamu Suleiman wanda aka yi wa satar yana kula da su har zuwa lokacin da hukuma za ta kai shi kotu. Ya ce wanda aka yi wa satar ne ya biya kudin allurai da karin ruwa da aka yi wa barawon, kuma da zarar ya samu sauki za su gabatar da shi a gaban kotu.