Mutanen kirki ne suka fi yawa a Najeriya – Janar Abdulsalam

Wakilinmu da ke Washinton DC kwanakin baya ya samu damar tattauwa da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar kan al’amura da dama da suka shafi Najeriya. Ga yadda hirar ta kasance: Aminiya: Ranka ya dade yaya kake ji yanzu da Najeriya ta samu sabon shugaba? Janar Abdussalam: Alhamdulillahi, sai godiya ga Allah Ubangiji da Ya […]

Mutanen kirki ne suka fi yawa a Najeriya – Janar Abdulsalam

Wakilinmu da ke Washinton DC kwanakin baya ya samu damar tattauwa da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalam Abubakar kan al’amura da dama da suka shafi Najeriya. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Ranka ya dade yaya kake ji yanzu da Najeriya ta samu sabon shugaba?

Janar Abdussalam: Alhamdulillahi, sai godiya ga Allah Ubangiji da Ya kaddara hakan ta faru, kuma ina kira ga jama’ar Najeriya da mu ci gaba da addu’a domin zaman lafiyar nan da aka samu ya dore.
Aminiya: Kwamitinku ya taka rawa wajen ganin an samu nasarar zabe cikin ruwan sanyi, me kake ji ya taimaka aka samu wannan lamarin cikin ruwan sanyi.?
Janar Abdussalam: Na farko dai sai mu gode wa Allah Subuhanahu wa Ta’ala, shi ne ya yi nasa mulkin, idan ka tuna lokacin da Kofi Ana (tsohon sakataren Majalisar dinkin duniya) shi da wadansu suka taru suka sanya Janar Buhari da Shugaba Jonathan suka yi yarjejeniyar zaman lafiya, bayan wannan zaman ne sai aka kafa kwamiti mu na zaman lafiya, to tun daga wannan lokacin muka shiga aiki, mu shiga nan, mu shiga can, muna tattaunawa da duk wanda muka ga yakamata har Allah cikin ikonSa ya sa aka yi zabe aka gama lafiya.
Aminiya: Wane irin aiki ne takamanme aka bai wa wannan kwamitin naku?
Janar Abdussalam: To ka san duniya tana zaton cewa tashin duniya ya zo lokacin zaben shekarar 2015 da za a yi a Najeriya, don haka kowa yana dar-dar a lokacin, idan ka lura, musammam kafin a yi zabe. Wannan ya sa kowa na komawa shiyyarsa, ‘yan Kudu sun koma gida, ‘yan Arewa da ke zaune a Kudu sun dawo gida, hatta bakinmu turawa kowa ya tattara komatsansa ya koma gida. Ana jira a ce an yi zabe a Najeriya kasar ta watse, sai Allah cikin ikonSa ya taimake mu. Wannan kwamitin namu yana ta tattaunawa da ‘yan siyasa da kowa da kowa don a yi zabe a lafiya. Mun tattauna da masu tsaron kasa, mun tattauna da su masu neman a zabe su, mun tattauna da su ‘yan siyasa, don dai a zauna lafiya.
Aminiya: Yanzu wane kallo kake jin duniya take wa Najeriya, ganin abin da ya faru game da wannan zaben?
Janar Abdussalam: To alhamdulillahi, tunda aka yi zabe aka gama lafiya hankali ya kwanta mutane yanzu suna kallon Najeriya da kima, cewa lallai Najeriyar nan yadda ake tsammaninta ba haka take ba, akwai jama’a maza da mata da yawa wadanda suka san abin da ya kamata kuma suka tabbatar aka yi zab,e lafiya aka gama lafiya, saboda haka Najeriya yau ta zame abin musali, ba ma a Afirka ba har a duniya gaba daya. Yadda shugaban da ke kan mulki ya fadi zabe ya kira wanda ya kada shi ya ce kai dan uwa ina maka murna, wannan zabe dai ka kada ni, ina taya ka murna, kuma Allah Ya ba ka sa’a.
Aminiya: Wadansu na cewa kiran shugaba Buhari da tsohon Shugaba Jonathan ya yi don taya shi murna an ce wai ku ne kuka nuna masa yayi haka, ina gaskiyar wannan batu?
Janar Abdussalam: Mutane dai kowa na fadin albarkacin bakinsa. Ko ma dai mene ne, yakamata a ce an yaba wa tsohon shugaba Jonathan, ya cancanci yabo na musammam saboda aikata abin da ya aikata, ko da ko wane ne ya ba shi shawarar yin hakan, domin ya kira Janar Buhari ya ce kai ka kada ni a zabe kuma Allah Ya taya ka riko, wannan ya cancanci yabo a ko’ina ne wannan mutumin yake, koda ko wani ne ya ce yayi hakan.
Aminiya: Wane kalubale ne yanzu a gaban Najeriya dangane da hadin kan ‘yan kasa?
Janar Abdussalam: Na farko sai mu kara gode wa Allah, domin ko wane dan Najeriya yana son zaman lafiya, da mun dauki wata turba wadda za ta kai mu ta baro, yanzu kowane dan Najeriya, na ciki da na waje, ya san amfanin zaman lafiya kuma ya ga hadarin da muka kusa shiga, don haka ko wane dan Najeriya a birni da kauye yana godiya ga Allah ganin yadda lamarin ya kasance, haka nan kuma yana son zaman lafiya, domin ko mun ki, ko mun so, dole muna bukatar juna, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, duka muna bukatar juna.
Aminiya: Ka san Shugaba Buhari a soja, ka san shi a farar hula, wane bambanci za ka ce yake da shi a wadannan rukunin biyu da ka sani?
Janar Abdussalam: To lokacin da Buhari ya yi mulkin soja kawo yanzu abubuwa sun canza, ba kamar da ba ne, saboda haka na tabbata Janar Buhari da farko ya yi minista, sannan ya zo ya yi gwamna, kana ya yi shugaban kasa, sa’ilin nan ya zo ya shiga siyasa, kuma ya tsaya takara har sau uku aka kada shi. Don haka cikin shekarun nan na tabbata Buhari ya canza, ya bi canjin lokaci, kuma ya koyi wadansu abubuwa da dama.
Aminiya: Wane irin canji kake sa ran ka ka gani yanzu?
Janar Abdussalam: To canji? Wai! Ka san mulkin soja da na farar hula daban suke, domin a mulkin soja kaine wuka, kaine nama, yanzu an zo ga mulkin siyasa, yanzu dole janar Buhari ya zamanto da nasa da ba nasa ba, dole sai ya ja kowa a jikinsa, kuma wajibi ne ya yi adalci, domin kowa abin da yake sa rai ke nan a yi, kuma hakan yakamata a yi.
Aminiya: Har yanzu wadansu na ganin zai dauki irin matakan nan nasa masu tsauri wurin mulki, kana ganin ya canja ba zai dauki irin wadannan matakan ba?
Janar Abdussalam: Ina fata wannan tsoron da ake ji ya sa Najeriya ta canza, domin mu ’yan Najeriya wani lokacin ba mu son sassauci, don haka ina fata Allah Ya sa wannan tsoron ya sa ’yan Najeriya su canza. Misali, daya daga cikin dabi’oinmu shi ne karya doka, sai ka ga direba ba ya da lasin na tuki amma sai ya dauki mota ya hau hanya, kuma ka ga yana tukin ganganci. Ina fata wannan tsoron ya sanya ’yan Najeriya su rika abu cikin tsari, su rika tunanin cewa kai yanzu Buhari fa ya zo, kowa ya shiga taitayinsa, to hakan zai sa abubuwa su canza.
Aminiya: A ganinka cikin matsalolin Najeriya wanne kake ganin yakamata ya fara karin kumallo da shi?
Janar Abdussalam: To akwai abubuwa da yawa, na farko shi ne tsaro, ya kokarta ya ga mun kwato kanmu daga wannan kalubalen da muke ciki, bayan tsaro sai kuma yadda za a yi a farfado da arzikin kasa, a samu yadda mutane za su daina yawon banza yadda za su samu aiki, yadda kowa zai wayi gari yana da inda zai tafi domin neman abin da zai ci.
Aminiya: Yaya kake ganin batun yaki da cin hanci da rashawa?
Janar Abdussalam: Wannan babban magana ce, domin tana da matsala ne, ba a Najeriya ba, a duniya ma gaba daya, don haka wannan matsalar kowane dan Najeriya yana da rawar da zai taka don ganin an yaki wannan annobar, idan dai ba a kashe ta gaba daya ba, to za ta ragu kwarai da gaske.
Aminiya: Wadasu na cewa zai yi wahala Buhari ya samu mutane irinsa da ba su da kashi a gindinsu domin ya yi aiki da su, kana jin zai iya samu?
Janar Abdussalam: To ko’ina a duniya akwai masu gaskiya akwai marasa gaskiya, kar ka manta fa Najeriya mu wurin sama da miliyan dari da saba’in ne, a ce duk cikin wannan adadin ba za a samu mutanen kirki ba, kai ka san wannan ba gaskiya ba ne wallahi ’yan Najeriya akwai na kirki fiye da yadda ba ka tsammani, ko’ina ka shiga za ka same su birjik, marasa kyau din ma kadan ne a Najeriya. Akwai mutane masu mutunci, masu daraja da sanin yakamata da hangen nesa, wadanda kasar ita ce a cikin zuciyarsu, marasa kirkin su ne suka samu dama har aka rika saninsu, amma a Najeriya ina mai kwarin gwiwar cewa akwai nagari da yawan gaske masu rike amana.
Aminiya: ’Yan Najeriya suna sa ran ya yi musu abubuwa da yawa, amma batu na gaskiya ba zai iya yin kome-da-kome ba, su mutane wace gudunmowa ya kamata su bayar?
Janar Abdussalam: Kamata ya yi shi janar Buharin ya fito ya fada wa ’yan Najeriya cewa abubuwan da kuke sa ran in yi fa sai kun taimaka mani, duniya ta san da haka. Misali, na farko dai Najeriya ina ne muke samun kudi? Mai ne, kuma man nan darajarsa ya fadi, domin haka abubuwa kamar su hanyoyi da makarantu da asibitoci da dai sauransu, ba za su canzu ba lokaci daya, mutane su gane cewa abubuwa sai a hankali za a iya canzu su, kuma ba duka ba, kamar yadda mutane suke tsammani.