Mutanen Kiru na neman agajin Gwamnatin Katsina

Al’ummar garin kiru da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina sun koka kan rashin kayayyakin inganta rayuwa a kauyen nasu wanda ke da tazarar akalla kilomita 21 daga babban birnin jihar. Mai magana da yawun al’ummar kauyen kiru Malam Ashafa Ukashatu ya shaida wa Aminiya a wani taro da suka yi domin nuna takaicinsu […]

Mutanen Kiru na neman agajin Gwamnatin Katsina
Mutanen Kiru na neman agajin Gwamnatin Katsina

Al’ummar garin kiru da ke karamar hukumar Rimi a jihar Katsina sun koka kan rashin kayayyakin inganta rayuwa a kauyen nasu wanda ke da tazarar akalla kilomita 21 daga babban birnin jihar.
Mai magana da yawun al’ummar kauyen kiru Malam Ashafa Ukashatu ya shaida wa Aminiya a wani taro da suka yi domin nuna takaicinsu kan yadda aka mayar da su saniyar ware, ya ce, “kimanin shekara 43 ke nan da kafa kauyen, amma har yanzu muna rayuwa kamar a cikin dajin rugu saboda rashin abubuwan da ya kamata a ce gwamnati ta wadata mu da su. Misali, ba mu da ruwan sha, ba mu da wajen da za a kula da lafiyarmu ko da kuwa dan karamin dakin shan magani ne, hanyar da muke bi muna zuwa cikin gari wadda ta taso daga Tashar-kadir kuma ba ta wuce kilomita hudu ba, sai a bara lokacin da aka kada gangar siyasa aka sanya wani burji da fitar da magudanun dalilin wani dan asalin gari mai suna Alhaji Abu Abdullahi.” ya ce aikin ma ya tsaya daga can bakin koramar da ke kusa da garin bayan kuma awon aikin ya wuce har wajen garin daga yamma. bayan sun yi zaton za a yi aikin hanyar za ta fito zuwa garin ’yargamji.
Malam Ashafa ya ce, aikin hanyar da ya biyo daga Tashar-kadir ya biyo ta bardaya zuwa tumbula ya shigo kiru, zai iya zarcewa zuka karare ya fita ‘yargamji kuma zai rage musu wahalhalu amma sai ya tsaya cik.
Malam Ashafa ya ce, baicin da allah ya kai musu liman isa, da ko ilimin addini ba su samu, saboda rashin makarantun zamani da na islamiyya. ya ce amma da zarar lokacin zabe ya zo sun fi kowa bayar da kuri’a bayan ko rumfar zaben ba su da ita, sai sun je maje ko wani wurin. “gaskiyar magana, mu a nan za mu iya cewa ba mu san ana gwamnati ba balle wani abin da ake kira jiha, da za a ce muna amfana da abin da take yi,” inji shi.
Malam Ashafa ya ce, da za su samu a datse musu ruwan damina ya zama karamin dam da mutanen da ke bardaya da’yarkadir da rijiya mai siminti da karni da rukudo zuwa nufawa da sun samu saukin karancin ruwan da suke fama da shi, amma yanzu sai sun yi tafiyar kilomita biyu zuwa uku kafin su debo ruwan da suke amfanin yau da kullum.
Malam Ashafa ya ce, dutsin da ake samu wajen gina rijiyar ya taimaka wajen fuskantar wannan matsala. “saboda haka muke rokon gwamnatin jihar katsina ta dubi kuncin rayuwar da muke ciki da ta hada da rashin wajen yin wata sana’a ko da a cikin gidajenmu, saboda ko wutar lantarki babu, babu wajen neman ilimi na zamani da islamiyya, ta taimake mu da duk abin da za ta iya yi.”