Mutanen Masarautar Saminaka sun saya wa kungiyar sintiri mota

Sakamakon sace-sacen da ake fama da shi a yankin masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna, mutanen masarautar sun saya wa kungiyar ’yan sintiri mota tare da gyara wa ’yan sandan yankin motarsu da ta lalace, domin tallafa wa jami’an tsaron wajen magance wannan matsala. Da yake mika wa kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta karamar Hukumar […]

Mutanen Masarautar Saminaka sun saya wa kungiyar sintiri mota

Sakamakon sace-sacen da ake fama da shi a yankin masarautar Saminaka da ke Jihar Kaduna, mutanen masarautar sun saya wa kungiyar ’yan sintiri mota tare da gyara wa ’yan sandan yankin motarsu da ta lalace, domin tallafa wa jami’an tsaron wajen magance wannan matsala.

Da yake mika wa kwamandan kungiyar ’yan sintiri ta karamar Hukumar Lere, Malam Zubairu Mustafa motar, Mai martaba Sarkin Saminaka Alhaji Musa Muhammad Sani ya bayyana matukar  farin cikinsa  kan wannan  tallafawa da masu halin yankin suka yi wa  jami’an tsaro don a magance sace-sacen da ake fama da shi a yankin.

Ya ce wannan kokari da aka yi zai sa gwamnati ta shigo ta tallafa wajen magance matsalar, inda ya  bukaci a hukunta duk wanda aka kama ya yi sata ko wani laifi a masarautar, koda dan wane ne  a hukumta shi kamar yadda doka ta ce. 

 Sarkin ya ce “Wadannan sace-sace da kashe-kashe ba za su kai mu ga nasara ba. Don haka ina kira ga al’ummar masarautar su rike sana’ar noma da aka sansu da ita.” 

A jawabin sakataren kwamitin duba matsalolin tsaro na masarautar kuma Talban Saminaka Alhaji Musa Mudi ya ce, Mai martaba Sarkin Saminaka ne ya kafa wannan kwamiti, ganin irin matsalolin tsaron da ake fama da su a yankin.

 Ya ce bayan da kwamitin ya gama bincikensa, sai manyan gari suka taru suka saya wa ’yan sintiri motar a kan sama da Naira miliyan daya, tare da  gyara wa ’yan sandan yankin motarsu da ta lalace. 

 Talban ya ce babban abin da ya sa al’ummar yankin suka yi wannan kokari, shi ne domin su nuna wa gwamnati cewa sun damu da abubuwan da suke faruwa na matsalar tsaro a  yankin, don haka suna son gwamnati ta dauki matakin magance matsalar.

Kwamandan kungiyar ’Yan sintirin ta karamar Hukumar Lere, Malam  Zubairu Mustafa  ya mika  godiyarsu kan wannan tallafin mota da aka ba su. Ya ce tallafi da aka yi musu ya nuna cewa al’ummar yankin sun fahimci muhimmancin aikin da suke yi. 

Sai ya ba da tabbacin cewa za su ci gaba da gudanar da ayyukansu na harkokin tsaro a yankin kamar yadda suka saba, inda ya yi kira ga al’ummar yankin su ci gaba da ba su goyon bayan da hadin kai wajen tona asirin duk wani bata garin da suka gani a yankin.