‘Mutanen miliyan 8 sigari za ta rika halakawa duk shekara’

Kididdigar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi, ya nuna cewa mutanen da za su mutu a duk shekara dalilin taba sigari zai kai miliyan takwas daga shekarar 2020.Wata kungiyar kare muhalli mai suna Enbiromental Rights Action Friends of the Earth, (ERA/FoEN) ce ta bayyana haka a Legas.Wani jami’in kungiyar ERA, Akinbode Oluwafemi ya […]

‘Mutanen miliyan 8 sigari za ta rika halakawa duk shekara’
‘Mutanen miliyan 8 sigari za ta rika halakawa duk shekara’

Kididdigar da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi, ya nuna cewa mutanen da za su mutu a duk shekara dalilin taba sigari zai kai miliyan takwas daga shekarar 2020.
Wata kungiyar kare muhalli mai suna Enbiromental Rights Action Friends of the Earth, (ERA/FoEN) ce ta bayyana haka a Legas.
Wani jami’in kungiyar ERA, Akinbode Oluwafemi ya bayyana a yayin wani taron manema labarai a Legas cewa a yanzu haka mutum miliyan shida ne ke mutuwa a duk shekara sanadin shan taba.
A cewar Oluwafemi hakan kuma ba laifin kowa ba ne illa kamfanonin taba da ke illa jama’a a Najeriya.
Ya bukaci Majalisar Dokokin ta kasa ta amince da kudirin dokar da aka gabatar mata da zai takaita amfani da sigari a kasar nan. “Ba za mu daina magana kan wannan kudiri da ke gaban majalisa ba har sai an amince da shi,” inji Oluwafemi.
Ya ce, “mutuwar da mutane ke yi dalilin shan sigari abu ne da za iya kauce masa muddin aka kudiri niyyar haka.”
A jawabin Daraktan kungiyar Kare Hakkin dan Adam da Sa ido a harkokin Majalisar Dokoki, Auwal Musa Rafsanjani, ya nanata bukatar a samar da dokar da za ta takaita yin amfani sigari musamman ta hanyar hana kamfanoni yin ta da kuma tallata ta.