Mutanen Moroko sun yi rub-da-cikin ta’aziyyar dan Siriya da ruwa ya ci
dimbin mutane a kasar Moroko sun tattaru a gabar kogin kasar don yin ta’aziyyar wani yaro dan shekara uku, mai suna Aylan Kurdi dan kasar Siriya da ya nutse a ruwa, inda daga bisani aka watso shi waje a rub-da-ciki. Masu ta’aziyyar sun rika yin rub-da-ciki a gabar ruwan da ke babban birnin kasar Rabat.Kafafen […]
dimbin mutane a kasar Moroko sun tattaru a gabar kogin kasar don yin ta’aziyyar wani yaro dan shekara uku, mai suna Aylan Kurdi dan kasar Siriya da ya nutse a ruwa, inda daga bisani aka watso shi waje a rub-da-ciki. Masu ta’aziyyar sun rika yin rub-da-ciki a gabar ruwan da ke babban birnin kasar Rabat.
Kafafen watsa labarai da shafukan sadarwa na intanet sun nuna hoton Aylan Kurdi a ringingine a kan wani tarin kasa da ake kira Bodrum, a wani wurin shakatawar ’yan yawon bude-ido da aka yi wa lakabin Firayiministan Turkiyya.