Mutanen Ningi ba su ga ci gaba ba
Cikin girmamawa, tare da fatan wannan wasika tawa za ta same ka cikin aminci da walwalar zuciya, ya mai girma Gwamna. Maigirma Gwauna tabbas mu al’ummar Ningi mun yi tsammanin ganin sauyi da samun cigaba fiye da lokutan baya, sai dai kash yau mune kusan karamar hukuma mafi koma baya a fannin auyukan cigaba a […]
Cikin girmamawa, tare da fatan wannan wasika tawa za ta same ka cikin aminci da walwalar zuciya, ya mai girma Gwamna. Maigirma Gwauna tabbas mu al’ummar Ningi mun yi tsammanin ganin sauyi da samun cigaba fiye da lokutan baya, sai dai kash yau mune kusan karamar hukuma mafi koma baya a fannin auyukan cigaba a Jihar Bauchi karkashin wannan gwamnati.
Maigirma gwamna a iya sanin mu kowanne gwamna ya hau yana kokarin nuna wa al’ummar ko wacce karamar hukumar cewa shi nasu ne, ta hanyar aiwatar musu da ayyukan cigaban yankinsu, wanda ko bayan ba ya nan za su iya nunawa tare da alfahari da shi.
Magana ta gaskiya mu al’ummar Ningi ba mu ga wani sahihin cigaba ba a karkashin gwamnatin ka ba, hasalima al’ummar Ningi mun fuskanci matsaloli da dama, kama daga matsalar zaizayar kasa da hanyoyin mu da suke kokarin yankewa da rashin ruwan sha a karkashin wannan gwamnati fiye da gwamnatocin baya wanda har yanzu muna fama da wadannan matsaloli dana zaiyano, shin a hakan ne mu al’ummar Ningi za mu yi alfahari da wannan gwamnati?
A halin da ake ciki yanzu karamar Hukumar Ningi ba ta da wakilin da a majalisar zartarwa a wannan gwamnati wan da zai iya tashi ya gabatar da bukatu da koken mu ga gwamnati yayin zaman majalisa, shin laifin me al’ummar Ningi muka yi wa wannan gwamnati ne?
A iya sanina dakuma nazarin da nayi gaba daya fadin Jihar Bauchi ba garin da aka nuna wa Maigirma Gwamna Abubakar M A soyayyar da al’ummar Ningi muka nuna masa amma kash yau mu ne saniyar ware kuma ‘yan bora a wannan gwamnati shin sakayyar da mu al’ummar Ningi muka cancanci a yi mana ke nan?
Yau duk mukaman da maigirma gwamna ya bayar a Jihar Bauchi ba wani dan Ningi da akaba wani ofishi na a zo agani da zai iya kawowa wannan gari namu cigaba, hakazalika idan ka zo
bangaren ayyukan cigaban al’umma a garin Ningi ba wani abin azo a gani da za ka nuna wannan gwamnati tayi, yau fa shekara biyu ke nan a madafun iko amma ba mu ga wani canji na cigaba ba illa cigaban mai ginin rijiya, amma duk yankin da ka je za ka ga dimbin ayyukan cigaba da ka yi masu kama daga tituna, makarantu,madatsun ruwa, da basu manyan mukamai a gwamnatin nan.
Maigirma gwamna kullum sai fada a ke yi kana aiki, amma karamar Hukumar Ningi ba ta shaida hakan ba, shin ina matsalar take ne? Maigirma gwamna kowa fa kan yi amfani da damar da ke hannunsa ne kafin ta kubuce masa, wannan karon damane gareka na share wa al’ummar ka hawayen da ya dade yana zuba m usu, Maigirma gwamna muna da dimbin matasan da suka kare makarantu da kyakkyawan sakamako, amma ba aikin yi, wanda muna tunanin da zuwanka za ka yi kokarin ganin ga share masu hawaye ganin irin rawar da matasan Ningi suka taka wurin kaiwa ga nasarar ka.
A karshe maigirma gwamnan acikin ladabi da girmamawa ina kira agareka da lokaci yayi da ya kamata ka waiwayo Ningi ka yi mana ayyukan da zai anfani al’umma, domin lokaci ya wuce da zamu rika yaudarar kan mu, muna cutar da kan mu da sunan kare muradun ka batare da fada wa juna gaskiya ba.
Cikin wannan shekaru biyu da suka rage ma a karagar mulki mu al’ummar Ningi muna bukatar ganin gagarumar cigaba wanda zai anfane mu dama wadanda zasu zo bayan mu anan gaba Insha Allah, galibin matsaloli da bukatun da Ningi ke da bukata kana da masanniya akai, muna fatan ganin sauyi a kai.
Muna kuma yimaka fatan Allah ya kara baka ikon kwatanta gaskiya da adalci a wannan mulki naka, Allah ya iyama da iyawarsa, Allah yayi maka jagora karya barka da dabararka, kyakkyawan manufofin da kegareka Allah yabaka ikon aiwatar dasu. Kukan Kurciya Jawabi ne.
Mudassir Maishayi Bakin Tasha Ningi,
Bauchi Najeriya
09025297045 Mudansir ibrahim <[email protected]>