Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya

Mutanen Potiskum da ke jihar Yobe sun yi ta murna da nuna godiya ga Allah bisa buxe babbar hanyar da ta ratsa garin wacce ta shafe sama da shekara uku a rufe.Rufe hanyar ya yi matuqar jawo koma-bayan harkokin kasuwanci a garin.Xaya daga mazauna garin Malam Gambo Barau wanda na daga cikin mutanen da suka […]

Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya
Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya

Mutanen Potiskum da ke jihar Yobe sun yi ta murna da nuna godiya ga Allah bisa buxe babbar hanyar da ta ratsa garin wacce ta shafe sama da shekara uku a rufe.
Rufe hanyar ya yi matuqar jawo koma-bayan harkokin kasuwanci a garin.
Xaya daga mazauna garin Malam Gambo Barau wanda na daga cikin mutanen da suka jajirce wajen kira ga hukuma ta buxe hanyar ya bayyana wa Aminiya cewa, a yanzu babu abin da za su ce illa godiya ga Allah, sannan suna godiya ga gwamna Ibrahim Geidam da Kwamishinan ’yan sandan jihar da Kwamandan sojoji dangane da qoqarin da suka yi na amincewa a buxe hanyar.
Ya roqi waxannan shugabanni su qara taimakawa a buxe hanyar da ta tashi daga fadar Mai Martaba Sarkin Fika zuwa hanyar Jos ta qetara kan hanyar Gombe saboda muhimmancinta ga harkokin sufuri.
Malam Gambo ya roqi jama’a su ba da haxin kai ga jami’an tsaro na kiyaye dokar fara amfani da hanyar daga qarfe 6 na safe zuwa qarfe 7 na yamma.
Alhaji Adamu Sani wani direba da ke jigilar fasinja daga Azare zuwa Potiskum cewa ya yi, kamar don su aka buxe hanyar domin a kullum sai ransu ya vaci in za su je tsohuwar tasha don sauke fasinja saboda sai sun bi ta lunguna maimakon su bi tsakiyar gari kai-tsaye.