Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya(1)

Mutanen Potiskum da ke jihar Yobe sun yi ta murna da nuna godiya ga Allah bisa bude babbar hanyar da ta ratsa garin wacce ta shafe sama da shekara uku a rufe.Rufe hanyar ya yi matukar jawo koma-bayan harkokin kasuwanci a garin.daya daga mazauna garin Malam Gambo Barau wanda na daga cikin mutanen da suka […]

Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya(1)
Mutanen Potiskum sun yi murnar bude babbar hanya(1)

Mutanen Potiskum da ke jihar Yobe sun yi ta murna da nuna godiya ga Allah bisa bude babbar hanyar da ta ratsa garin wacce ta shafe sama da shekara uku a rufe.
Rufe hanyar ya yi matukar jawo koma-bayan harkokin kasuwanci a garin.
daya daga mazauna garin Malam Gambo Barau wanda na daga cikin mutanen da suka jajirce wajen kira ga hukuma ta bude hanyar ya bayyana wa Aminiya cewa, a yanzu babu abin da za su ce illa godiya ga Allah, sannan suna godiya ga gwamna Ibrahim Geidam da Kwamishinan ’yan sandan jihar da Kwamandan sojoji dangane da kokarin da suka yi na amincewa a bude hanyar.
Ya roki wadannan shugabanni su kara taimakawa a bude hanyar da ta tashi daga fadar Mai Martaba Sarkin Fika zuwa hanyar Jos ta ketara kan hanyar Gombe saboda muhimmancinta ga harkokin sufuri.
Malam Gambo ya roki jama’a su ba da hadin kai ga jami’an tsaro na kiyaye dokar fara amfani da hanyar daga karfe 6 na safe zuwa karfe 7 na yamma.
Alhaji Adamu Sani wani direba da ke jigilar fasinja daga Azare zuwa Potiskum cewa ya yi, kamar don su aka bude hanyar domin a kullum sai ransu ya baci in za su je tsohuwar tasha don sauke fasinja saboda sai sun bi ta lunguna maimakon su bi tsakiyar gari kai-tsaye.