Mutanen Sabon Gida sun koka kan wurin da za a gina Jami’ar Tarayya a Zamfara
Jama’ar garin Sabon Gida da ke Jihar Zamfara sun koka, kan labarin da suka samu game da auna gonaki da gidajensu da aka yi a baya don samar da matsugunin Jami’ar Tarayya inda har yanzu ba a biya su ba.Koken nasu ya biyo bayan labarin da suka samu ne cewa yanzu an sake auna wurin, […]

Jama’ar garin Sabon Gida da ke Jihar Zamfara sun koka, kan labarin da suka samu game da auna gonaki da gidajensu da aka yi a baya don samar da matsugunin Jami’ar Tarayya inda har yanzu ba a biya su ba.
Koken nasu ya biyo bayan labarin da suka samu ne cewa yanzu an sake auna wurin, amma ban da gidajensu sai dai gonakinsu, wanda hakan ya sake jefa su cikin damuwa, kamar yadda Sarkin Fulanin Unguwar Alhaji Mande ya bayyana wa wakilinmu.
Ya ce “Mun gamsu da kwamitin Injiniya Rabi’u Sa’idu Moriki da ya zo ya auna gidaje da gonakinmu, wadanda suna cikin farfajiyar jami’ar, amma sai ga shi daga baya wani Darakta daga Ma’aikatar kasa da Safiyo Injiniya Bello Maude ya zo ya ce mana, wai an cire gidajenmu, sai dai gonakinmu ne za su shiga cikin awon, wannan abin ya daure mana kai.”
Ya ce idan Bafillace ba shi da gona kusa shi ina zai a je dabobinsa? Ya ce Bafullatani ba ya zama inda babu gona kusa da shi, “Yanzu an saye gonakinmu, ina za mu sa dabobinmu? Don haka muna kira ga Gwamnatin Zamfara da ta Tarayya su taimaka a yi amfani da tsarin farko na kwamitin Injiniya Rabi’u Moriki a saye gidajenmu da gonakinmu gaba daya, sai mu tsallaka wani bangaren mu sayi wani, inji Sarkin Fulani.
Ya yarda, sai dai mun ji an ce an sake sanya wasu mutane don bin diddigin aikin da muka yi a baya.”
Kwamishinan kasa da Safiyo Injiniya Lawal Jangebe ya ce an samu canjin alkaluma daga na kwamitin farko wanda ya ce za a biya Naira miliyan 680.
Jangebe ya ce “Ma’aikatarsu ce ta ba Injiniya Moriki aiki kuma tana da ikon sanya wasu su bi kadin aikin. Kuma batun fitar da wasu gidaje da gidajan mai, sun ga amfanin al’umma zai yi shi ya sa suka yi haka, kuma sakamakon fitar da gidajen gwamnati za ta biya diyyar Naira miliyan 420 da za a fara nan ba da jimawa ba.”