Mutanen Saudiyya na gudu daga birane zuwa kauyuka
Mutanen Saudiyya da dama sun fara barin manyan biranen kasar suna komawa yankunan karkara da kauyukansu na asali da zama sakamakon karancin kudin haya da wadatattun ayyukan yi da kuma cikakkiyar kula da lafiya da samun ingantaccen ilimi a can. Jaridar Arab News wadda ta ruwaito haka a ranar Talatar da ta gabata ta ce […]
Mutanen Saudiyya da dama sun fara barin manyan biranen kasar suna komawa yankunan karkara da kauyukansu na asali da zama sakamakon karancin kudin haya da wadatattun ayyukan yi da kuma cikakkiyar kula da lafiya da samun ingantaccen ilimi a can.
Jaridar Arab News wadda ta ruwaito haka a ranar Talatar da ta gabata ta ce mutanen Saudiyyan da ke komawa karkara da kauyukan sun kuma ce yankunan sun fi samar da rayuwa mai inganci fiye da manyan birane da ke cike da cinkoso. Sannan ga karancin wahalhalu, kuma ’ya’yansu za su taso a yanayi mai kyau tare da saukin ganawa da dangi da abokansu.
daya daga cikinsu mai suna Khalaf Al-Dosari, da yake aiki da wani gidan watsa labarai ya ce: “Tashinsa daga birnin Riyadh zuwa Wadi Al-Dawasir wata shawara ce da ta dace. Cinkoson ababen hawa da matsuwa a gidaje da mugun tsadar gidan haya sun tilasta iyalai da dama barin birnin Riyadh.”
Ya ce kananan garuruwa ba su da cinkoson ababen hawa, kuma suna da yanayi mai kyau da karancin kashe kudi don rayuwa. Sai ya bukaci gwamnati ta karfafa musu gwiwa ta hanyar gina manyan asibitoci da manyan shagunan kasuwanci tare da gudanar da bukukuwa da nune-nunen kayayyaki da kasuwannin duniya.
Shi kuwa Mohammed Al-Mater, wanda ya bar birnin Dammam zuwa wani kauye da ke Al-Ahsa, ya ce lokacin da yake aiki a birni, sun ci gaba da zama a gida. “Iyalaina ba su son barin kauye zuwa babban birni. Na yi ta fama da damuwa saboda wahalar zuwa da dawowa kullum.”
Abdulwahab Al-Manna kuwa cewa ya yi ya bar birnin Dammam ne zuwa kauyen Al-Nairiyah domin kauce wa cinkoson ababen hawa, kuma tsadar rayuwa ta tilasta masa ya rika tashi da sassafe domin zuwa aiki. Ya ce baya ga haka ya yi nesa da iyalinsa, amma yanzu ya fi ji dadi da ya koma kauyensu inda yake ziyartar Dammam da Alkhobar a duk lokacin da yake bukata.
Shi kuwa Mohammed Al-Shamrani cewa ya yi ya bar birnin Dammam ne zuwa kauyen Asir saboda an fi samun kwanciyar hankali a kauye. Ya ce akwai kayayyakin more rayuwa da wuraren nishadi a kauyensu.