Mutanen Sudan zama lafiya ya fi zama dan sarki

Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya, ina yi wa daukacin Ma’aikatanku fatar alheri. Ku ba ni dama a yau domin in yi tsokaci dangane da abin da ke ci gaba da aukuwa a kasar Sudan, kasar da zaman lafiya a yanzu ke kan siradi a cikinta. A zahirin gaskiya dai babban abin bakin ciki ne da […]

Mutanen Sudan zama lafiya ya fi zama dan sarki
Mutanen Sudan zama lafiya ya fi zama dan sarki

Assalamu alaikum Editan Jaridar Aminiya, ina yi wa daukacin Ma’aikatanku fatar alheri. Ku ba ni dama a yau domin in yi tsokaci dangane da abin da ke ci gaba da aukuwa a kasar Sudan, kasar da zaman lafiya a yanzu ke kan siradi a cikinta.

A zahirin gaskiya dai babban abin bakin ciki ne da alhinin jin irin abubuwan assha da ke ci gaba da faruwa na tarzoma da asarar rayuka a kasar sakamakon kiki-kakar da ke tsakanin farar hula da gwamnatin sojin kasar, wadda kuma ya samu armashin kafafen watsa labaran kasashen ketare.

Kirana ga talakawa al’ummar kasar Sudan shi ne, su kai zukatansu nesa, su toshe kunnuwansu daga duk wata ziga da za ta tunzura su har su yi bore wa sababbin shugabanninsu, wadanda suka gaji mulki daga farar hular da suka yi sanadiyyar tumbukewa a dalilin tsadar burodi a wancan lokaci. Domin kaucewa yin da-na-sani daga baya. Su kuma sani cewa fa duk abin da zaman lafiya ya gaza kawowa, to fa tashin hankali ba zai ta taba kawo shi ba. Haka kuma hanyar lafiya da shekara akan bi ta. Domin kuwa shi mahakurci mawadaci ne. Don haka zama lafiya ya fi zama dan Sarki.

Daga karshe ina fata za a sake zama kan teburin sulhu a tsakanin shugabannin mulkin sojin kasar Sudan da  shugabannin farar hular kasar domin lalubo hanyar warware wannan zare da ya zarge wannan kasa a bangaren shugabanci.  Da fatar Allah Ya zaunar da kasashenmu na Afirka lafiya, Ya kuma kare kasashenmu daga aukawa cikin tarkon duk wani ko wata mai hassada a yayin da ya yi hassada.  Amin.

Daga Injiniya Shamsuddeen Abdullahi Rijau.

 07081235949