Mutanen Yobe sun ji dadin bude hanyar Damaturu zuwa Biu

A ranar Asabar da ta gabata ne mafarkin al’ummar Jihar Yobe musamman na garin Buni Yadi ya tabbata bayan da aka sake bude musu hanyar Damaturu zuwa Buni Yadi zuwa Biu a Jihar Borno mai nisan kilomita 132. Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Buratai ne ya sake bude hanyar a wani biki da aka […]

Mutanen Yobe sun ji dadin bude hanyar Damaturu zuwa Biu
Mutanen Yobe sun ji dadin bude hanyar Damaturu zuwa Biu

A ranar Asabar da ta gabata ne mafarkin al’ummar Jihar Yobe musamman na garin Buni Yadi ya tabbata bayan da aka sake bude musu hanyar Damaturu zuwa Buni Yadi zuwa Biu a Jihar Borno mai nisan kilomita 132.
 Babban Hafsan Sojin kasa Laftana Janar Tukur Buratai ne ya sake bude hanyar a wani biki da aka gudanar a garin Buni Yadi.
Laftana Janar Tukur Buratai ya nanata kudirin rundunar sojin kasar nan na kakkabe ’yan ta’addan Boko Haram, inda ya ce saura kiris a kawo karshensu.
Janar Buratai ya ce harkokin tsaro suna inganta a yankin Arewa maso Gabas kuma hakan ne ya ba shi karfin gwiwar bude hanyar saboda muhimmancinta ga ci gaban tattalin arzikin yankin.
Ya yi fatar bude hanyar zai sake bude wani sabon babi ga harkokin kasuwanci da sufuri da noma da kiwo da sauran harkokin rayuwar al’ummar yankin. Kuma ya roki gwamnatin Jihar Yobe ta taimaka ta gyara hanyar don ba da dama ga al’umma su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin sauki.
A jawabin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam wanda Kwamishinan Ayyuka Alhaji Muhammad Siraja Wakil ya wakilta, ya mika godiya ne ga jamil’an tsaro kan dawo da zaman lafiya a yankin wanda ya sa aka sake bude hanyar wadda ta dauki lokaci a rufe.
Ya ce gwamnatin jihar za ta matsa wa kamfanin da ke aikin gyaran hanyar da rashin zaman lafiya ya tilasta shi dakatar da aikin, ya gaggauta dawowa don ci gaba da aikin.
Shugaban riko na karamar Hukumar Gujba Alhaji Kyari Batarama ya nuna jin dadin al’ummar yankin kan bude hanyar, inda ya ce hakan zai farfado da tattalin arzikin al’ummarsa da aksarinsu manoma ne da ’yan kasuwa.
Da Aminiya ta tuntunbi wani kusa a kungiyar Direbobi ta kasa (NURTW) reshen Buni Yadi, Malam Bashari Mai Daura, ya ce bude hanyar ya yi musu dadi, sai dai  illa abin da ya bukaci gwamnatin jihar da ta tarayya su taimaka su gyara hanyar, kuma gwamnati ta kawo musu dauki don gyara gidajensu da kuma samar musu abinci da jari don saukaka musu kuncin da suke ciki.