Mutanen Zuntu sun koka kan farmakin sojoji

Mutanen garin Zuntu da ke Karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna sun bukaci gwamnati ta binciki yadda sojoji suka mamaye garin tare da yin harbe-harben da suka yi sanadaiyyar mutuwar wani matashi. Wata majiya ta ce harbin ya samu matashin mai suna Aliyu Alaramma dan shekara 17 a kirji ne, sakamakon wata hatsaniya a lokacin […]

Mutanen Zuntu sun koka kan farmakin sojoji
Mutanen Zuntu sun koka kan farmakin sojoji

Mutanen garin Zuntu da ke Karamar Hukumar Kubau a Jihar Kaduna sun bukaci gwamnati ta binciki yadda sojoji suka mamaye garin tare da yin harbe-harben da suka yi sanadaiyyar mutuwar wani matashi.

Wata majiya ta ce harbin ya samu matashin mai suna Aliyu Alaramma dan shekara 17 a kirji ne, sakamakon wata hatsaniya a lokacin zaben fid da gwani da ya gudana na dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna na Jam’iyyar APC a ranar Lahadi 7 ga Oktoba. Wata takardar koke da mai magana da yawun al’ummar garin, Barista Suleiman Mohammed Zuntu ya sanya wa hannu, mutanen garin sun koka kan yadda sojoji suka shiga garin duk da cewa akwai ’yan sanda a wurin, amma suka yi ta harbin kan mai uwa da wabi kan al’umma.

A cewar takardar, al’ummar Zuntu sun nuna takaicinsu bisa yadda sojojin suka shiga suka fara harbe-harbe tare da kame musu mutane.

A lokacin da Aminiya ta ziyarci garin na Zuntu ta tarar da malamin marigayin wanda almajiri ne, mai suna Alaramma Usman baya gida ya tafi garinsu don  sanar da mahaifinsa yadda  sojojin suka harbe Aliyu.

To amma daya daga cikin almajiran malamin da sojojin suka kama suka tafi da su ofishinsu ya bayyana halin da suka shiga a hannun sojojin bayan kashe musu dan uwa.

“Almajirin namu yana sana’ar sai da rake a bakin titi. A lokacin da aka harbe shi mun dauke shi zuwa wani asibiti da ke kusa damu a kan babur, suka ce ba za su iya ba, sai muka fara shawarar yadda za mu yi, nan take rai ya yi halinsa, sai muka dawo da shi gida, mun shimfidar da shi ke nan sai sojojin suka shigo inda muke suka hau mu da duka da tsawa suka kama mu  tare  da malamanmu gaba daya suka ta fi da mu ofishinsu a garin Anchau, suka tsare mu kwana guda suna ta dukanmu. Da gari ya waye suka sa mu noma tare da yi mana wulakanci, sannan suka hana mu yin Sallah, kuma mun bar gawa a kwance a daki cikin jini sai da misalin karfe 12 na rana sannan aka sake mu, kafin ’yan sanda su zo su yi bincike sannan aka ba mu dama muka yi jana’izar marigayin.

DPO din yankin Pambeguwa ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ya sanar da babban ofishinsu na Kaduna, kuma ana ci gaba da tattara bayanai kan abin da ya haifar da matsalar don magance faruwar haka a gaba.

Game da cewa sojoji sun far wa ’yan sanda da duka da jama’ar garin Zuntu, wani dan sanda da bai so a ambaci sunansa ba da ke cikin wadanda suka yi sintiri a ranar da lamarin ya faru, ya ce babu wani dan sanda da sojoji suka doka domin sun riga sun kwantar da tarzomar  a garin Zuntu sun wuce, domin ci gaba da zirga-zirga don kara tabbatar da zaman lafiya sai suka samu labarin cewa wadansu sojoji sun far wa garin sun harbi  yaro daya ya rasu.

Shugaban Karamar Hukumar Kubau, Alhaji Sabo Aminu ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da abin ya faru suna Zariya wajen zaben fid da gwani sai daga baya ya sami labarin abin da ya faru.

Alhaji Sabo ya bayyana juyayinsa bisa wannan lamari ya kuma bayyana garin Zuntu a matsayin garinsa bisa la’akari da yadda suka jajirce wajan zabensa a matsayin shugaban karamar hukumar, dan haka ba zai taba yarda ko yasa a cautar da wani a garin ko al’ummar Karamar Hukumar Kubau ba a matsayinsa na shugaba. Haka kuma wakilinmu ya tuntubi Kakakin Rudunar ‘Yan Sanda Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ta waya tare da tura masa sakon kar-ta-kwana amma har zuwa hada wannan rahoto ba bu amsa.