Mutanena sun dandan kuda a hannun Boko Haram – Kukuwa
dan Majalisar Jihar Yibe mai wakiltar mazabar Gulani Alhaji Abdullahi Usman Kukuwa ya bayyana cewa al’ummar mazabarsa sun rika dandana kudarsu a hannun sakamakon kungiyar Boko Haram kasancewar yankinsa na cikin yankunan da ’yan kungiyar Boko Haram suka kwace a baya.Alhaji Usman Kukuwa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya […]
dan Majalisar Jihar Yibe mai wakiltar mazabar Gulani Alhaji Abdullahi Usman Kukuwa ya bayyana cewa al’ummar mazabarsa sun rika dandana kudarsu a hannun sakamakon kungiyar Boko Haram kasancewar yankinsa na cikin yankunan da ’yan kungiyar Boko Haram suka kwace a baya.
Alhaji Usman Kukuwa ya bayyana haka ne lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu, inda ya ce kasancewar ’yan Boko Haram sun kwace yankin ya koma karkashinsu a baya akasarin mutanensu sun yi gudun hijira.
Ya ce sun gode wa Allah da Ya arzurta al’ummar kasar nan da Shugaban kasa mai kyakkyawan kudiri ga kasar nan, inda ya roki Gwamnatin Tarayya ta samar da ingantaccen tsaro da zai sa al’ummomin su samu natsuwa da kwanciyar hankalin da za su gudanar da harkokin rayuwarsu tare da samar musu da takin zamani don zuba wa gonakinsu.
“Babbar fatata ita ce Allah Ya wuce wa sababbin hafsoshin tsaron kasar nan gaba don samun nasarar murkushe ’yan ta’addan da suka addabi yankin Arewa maso Gabas, kuma da yardar Allah nasara na gab da samuwa bisa ga alamun da suke bayyana a yanzu,” inji shi.
Alhaji Usman Kukuwa ya yaba wa al’ummar mazabarsa kan ba shi dama a karo na uku, inda ya ce kwarin gwiwar da yake samu daga jama’arsa yana karfafa shi wajen jajircewa don yi musu wakilcin da ya dace, inda ya ce zai ci gaba da barinsa kofarsa a bude ga jama’arsa dom karbar shawarwari da koke-kokensu.