Mutfwang ya rantsar da zaɓaɓɓun Shugabanni qananan hukumomi 

Gwamnan Filato ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar Filato 15 a cikin 17 da ake da su a jihar.

Mutfwang ya rantsar da zaɓaɓɓun Shugabanni qananan hukumomi 

Gwamnan Jihar Filato Barista Caleb Mufwang ya rantsar da zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomin jihar Filato 15 a cikin 17 da ake da su a jihar.

Gwamnan ya rantsar da zavavvun Shugabanni qananan hukumomin ne, a daren jiya Alhamis a gidan gwamnatin Jihar da ke garin Jos.

Sababbin ciyamomin da aka rantsar sune Steven Gyang Pwajok, Barikin Ladi, Dokta Joshua Sunday Riti, Bassa, Amanalau John, Bokkos, Barista J.K Chris, Jos ta Arewa, Silas Patrick Dung, Jos ta Kudu, Markus Ussaini Nyam, Jos ta Gabas, Salihu Ayuba Musa, Kanam.

Sauran sune Lapching Ezekiel, Kanke,

Nanfa Alhassan Jingfa, Langtang ta Kudu, Emmanuel Bala, Mangu, Benard Alkali, Mikang, Christopher Audu ma, Quan pan, Bature Sati Shuwa, Riyom,

Kemi Nicholas Nshe, Shendam da kuma Hamisu Anani Muhammad, Wase.

Da yake jawabi a wajen Gwamna. Caleb Mufwang ya taya sababbin shugabannin murnar zaɓen su da aka yi.

Ya yaba wa hukumar zaɓen jihar kan yadda ta gudanar da zaɓen a kan gaskiya da adalci.

Don haka, ya yi alqawarin baiwa zaɓaɓɓun shugabanni cikakken goyon baya da hadin kai wajen gudanar da ayyukan su.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya