Mutfwang ya samu tikitin tazarce na Gwamnan Filato
Shugaban kwamitin zaben, Mista Fidelis Mnyim, ya sanar cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya sami kuri’u 233, 335
Gwamna Barista Caleb Mutfwang, ya lashen zaben fid-da-gwani na takarar kujerar Gwamnan Jihar Filato, karkashin jam’iyyar APC a zave mai zuwa na shekara ta 2027.
Gwamnan ya lashe wannan zaben ne, bayan da aka kammala tattara sakamakon daga dukkan kananan hukumomin jihar 17.
Da yake bayyana sakamakon zaven, a daren Juma’a a garin Jos, Shugaban kwamitin zaben, Mista Fidelis Mnyim, ya sanar cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya sami kuri’u 233, 335, a yayin da abokin takararsa, Kwamanda Yilchini Bida Mai ritaya ya sami kuri’u 3,070.
Don haka, ya ayyana Gwamna Mutfwang, a matsayin wanda ya nasara.